Jami'an kotu sun tsallake rijiya da baya a kasuwar yan lemu Maraba jihar Nasarawa.
Jami'an kotu sun tsallake rijiya da baya a kasuwar Ƴan lemo dake garin maraba a jihar Nasarawa.
A ranar Talata 16 ga watan Mayun 2023 ne wasu fitsararru da ake zaton Masu gadin kasuwar ne su duki jami'an kotu da wasu mutum biyu.
Lamarin ya faru ne bayan bada umarni da Kotun High Court 3 dake garin maraba tayi na a liƙa takardun bukatar kara wasu kungiyoyi biyar da suke gudanar da kasuwanci a kasuwar ta Yan lemo.
Wace za'a gabatar da zaman a ranar 30 ga wannan watan na Mayu.
Sai dai jaridar Eyeshadow ta rawaito cewa, ana zargin Sarkin Hausawan maraban Gurku da Alhaji Baba Ali Nana da hannu cikin dukan jami'an Kotun.
An tsinkayi wata sauti na muryar Sarkin Hausawan maraban yana jan kunnen wani Jami'in kotu inda yake masa barazanar zaisa a kore shi a mayar da shi ƙauye da aiki.
Haka zalika sarkin Hausawan maraban Alhaji Usman Mani din anji inda yake faÉ—awa Jami'in Kotun cewa akwai yan giya da yan kwaya (Yan shaye-shaye) a kasuwar ta yan lemo, saboda haka yayi hankali.
Post a Comment
0Comments