Fitaccen Dan Jarida kuma Dan kasuwa Ahaji Sani Ahamad Zangina ya maka Shugaban kasuwar Yan Lemo Kuma Dan majalisa Mai wakilatar mazabar keffi ta yamma Hon. Baba Ali a gaban kotu.
Wani Fitaccen mai harkar filaye da gidaje ne a garin Maraba Alhaji Sani Ahamad Zangina ya maka Dan majalisar a gaban kuliya.
A yau 26 ga watan afrailu ne aka cigaba da sauraron karar da Alhaji Sani Ahamad Zangina dake garin Maraban gurku ya maka Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Shiyar Keffi ta yamma a jihar Nasarawa.
Mai kara Alhaji Sani Ahamad Zangina ya shigar da karar yana bukatar kotu ta karba masa filinsa Wanda a halin yanzu shine wasu ke zaune suke kasuwanci a cikinsa.
Mai kara Alhaji sani Ahamad Zangina yayi zargin cewa ana masa barazanar kisa akan filin. Ba sau daya ko sau biyu ba. Hatta a zaman kotun da aka gabatar a yau Kafin fara zaman kotun sai da aka masa barazanar cewa za’a masa yankar rago.
A Cewarsa. Mai kara Alhaji Sani Ahamad Zangina ya bukaci kotun High court dake garin maraba da ta dakatar da yan kasuwa masu sauke kaya a kasuwar yan lemun har sai an kammala yin Shari’a a wajen.
Inda ya bukaci duk wani kaya da za’a sauke a kasuwar a garzaya dashi zuwa babbar kasuwar karu na Muhammadu Buhari International Market Kafin a kammala Shari’ar, ko kuma duk wani kudin shiga na kasuwar na haraji a kawo shi gaban kotu har sai an kammala Shari’ar.
An bayyana haka ne a wata takarda mai dauke da Sanya hannun mai karar wadda za’a saurara ranar 30 ga watan Mayu na shekarar 2023.
In har kotu ta gamsu da bukatar mai karan toh hakan yana nufin ko dai kasuwar ta tashi kenan zuwa Muhammadu Buhari International Market wadda Zangina ke zargin mai karar da kasancewa daya daga cikin wadanda suka hana kasuwar rawar gaban hantsi, saboda biyan bukatar wasu tsiraru.
Kotu ta sanya ranar 15 ga watan Mayu a matsayin ranar cigaba da sauraren ƙarar a babban kotu dake karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.
Post a Comment
0Comments