An gano dalilin tashin kayan Abinci a Najeriya karanta a tsana ke – YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0


 Farashin masara ya yi tashin gwauron zabi daga farkon watan June zuwa yanzun da na ke rubutun nan. A farkon watan June an sayar da masara N22k, amma a wannan watan farashin masarar ya cilla har zuwa N44k. ma’ana, daga watan da ya gabata zuwa yanzun farashin ya ninka sau biyu.

Kamar yadda ku ka sani babu abin da ke faruwa ba tare da dalili ba, haka ma tashin farashin da masarar ya yi ya faru ne bisa dalilai na kusa da na nesa. Idan na ce dalilai na kusa, to ina nufin dalilan da suka faru kwanan nan. Idan kuma na ce dalilai na nesa, to ina nufin abin ya faru a baya wanda kuma ya taimaka wajen tashin farashin masarar.

Daga cikin dalilan da suka haifar da tashin masara akwai:

  1. YANAYIN DAMUNA

Tashin farashin kayan abinci a lokacin damuna ba sabon abu ba ne a Nigeria, domin a kowace da damuna kayan abinci su kan tashi. Saboda normally kayan abinci suna yin karanci a hannun Manoma a lokacin damuna, sakamakon Manoma sukan sayar da abinda suka noma a damuna domin su sayi kayan noma (taki da feshi), biyan kudin zirga-zirga da kuma biyan kudin masu aiki. A Nigeria mafi yawan Manoman sukan sayar da kayan da suka noma ne tun farkon shigar damuna, idan damuna ta yi nisa kuma sai a samu karanci kayayyakin noma a kasuwa.

Wannan ma ina magana ne akan manoman ma da ke iya barin kayan abinci har ya kawo damun domin su sayi taki da feshi, ballantana mafi yawan manoma a Nigeria suna noma iya abin da za su ci ne. Wasu kuma tun kaka su ke sayar da abin da suka noma. To idan damuna ta zo sai ka ga Manoma da wadanda ba manoma duk yanzun sayen kayan abinci su ke, hakan ne ke haifar da yawan masu bukatar sayen kayan abincin (Demand) yayin da kuma a kasuwa kayan abincin na karanci (Supply). Tunda supply na kayan abinci ya yi karanci sannan kuma demand na kayan abinci ya karu, to babu makawa sai an samu tashin farashin kayan abincin. Wannan shi ne dalilin da ya sa a kowacce shekara kayan abinci ke yin tsada a lokacin damuna.

  1. CHANJIN KUDI

Chanjin kudade da aka yi a watan February da ya gabata, wanda ya haifar da karancin sabbin kudade a hannun al’umma ciki har da Manoma ya taimaka wajen haddasa tashin farashin kayan abinci. Domin Manoma su samu sabbin kudade sun dinga fitar da kayan da suka noma suna sayarwa a farashi mai sauki, wanda hakan ya janyo Manoma sun sayar da kayan abincinsu fiye da kima. Saukin da kayan abinci ya yi a lokacin, ya janyo Yan kasuwa sun amfana da saukin farashin wajen sayen adadi mai yawa na kayan abinci suna ajewa. Ma’ana dai, da yawan kayan abinci ya bar hannun Manoma sun koma hannun Yan kasuwa. Idan haka ta faru kuwa, to dole zuwa gaba a fuskanci tashin farashin kayan abincin sosai. To yanzun gaban har ta zo, don haka ne farashin masara ya tashi.

  1. FADUWAR DARAJAR NAIRA DA TASHIN DOLLAR

Faduwar darajar Naira a kan dollar da ya faru tun daga watan da ya gaba zuwa yanzun yana daga cikin dalilin da haifar da hauhawar farashin masara. Tun da dollar ta yi mahaukacin tashi sakamakon cire hannun gwamnatin wajen saita farashin dollar din da gwamnatin Tunubu ta yi, to dole kayan noman da Manoma ke amfani da su kamar taki da feshi su yi tsada. Dama kuma Manoma da yawa sun dogara ne wajen sayar da abin da suka noma domin sayen taki da feshi. Tun da sun tashi, to dole kayan abinci ma ya tashi.

Bayan haka, tashin darajar dollar a Nigeria zai shafi tashin kayayyaki masarufi gaba daya, a ciki har da masarar ita kanta. Wani zai ce ai ita masara a Nigeria a ke noma ta don haka tashin dollar bai kamata ya shafe ta ba. Wannan gaskiya ne, amma yan Nigeria na da dabi’ar kara kudin kayayyaki da zarar su ka ji dola ta tashi, kuma koda kayayyakin ba su bukatar amfani da dolar domin sayensu.

  1. CIRE TALLAFIN MAI:

Ita ma masara kamar sauran kayayyakin gona ta ke ana sayen ta ne a hannun Manoma, su kuma Manoman mafi yawansu suna kauyuka. Ashe kuwa, domin masara ta kai ga kasuwa dole tana bukatar daukar ta a motoci ko mashina. Daga kasuwa kafin akai masarar zuwa garuruwa nan ma dole a yi amfani da abubuwan zirga-zirga.

Mafi yawan abubuwan zirga-zirgar da mu ke amfani da su domin daukar kayan abinci suna amfani ne da Fetur, shi ya sa tsadar da fetur din ya yi sakamakon cire tallafin mai dole zai haddasa tashin farashin kayayyakin gona ciki har da masara. Baya ga haka, yan Nigeria suna da dabi’ar kara kudin mota da zarar fetur ya tashi, hatta motocin da ba sa amfani da fetur za ka ga suna kara kudin da zarar suka ji fetur ya tashi.

Wani zai ce to mai ya sa masara ce farashinta ya yi saurin tashi a halin yanzu? Saboda a halin yanzu ita ce kayan abincin da talakawa suka fi amfani da ita, a Nigeria kuma kashi 70 na mutane talakawa ne.

Idan mai karatu na lura, zai ga abubuwa da yawa ne suka hadu su ka zama silar tashin farashin masara fiye da kima. Kuma ma dama a duk lokacin da ka ga farashin abu ya tashi to ba abu daya ne kawai ke haifar da shin ba. Gwargwadon yawan abubuwan da suka haifar da shin, gwargwadon yawan da farashin zai yi idan ya tashi.

Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!