Tura dalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare, daɓen kwalo ne kawai - APC
Babbar jam'iyyar adawa ta APC a jihar Kano, ta soki tsarin tura dalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare domin yin karatun digiri na biyu a fannonin ilimi daban daban, inda tace daɓen kwalo ne kawai, domin babu bukatar hakan a halin yanzu.
Kakakin jam'iyyar, Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana haka, inda yace anfi bukatar a inganta ilimin cikin Gida kafin a tafi ƙasashen ƙetare, saboda haka basu gamsu da wannan tsari ba, domin daga baya ma za'a iya jiyo koke-koken daliban akan batun kuɗin makaranta.
A ranar Juma'a ne dai rukunin farko na daliban da suka fita da sakamakon mafi kyau a karatun digirin farko yan asalin jihar Kano, suka tashi zuwa ƙasar India domin karatun digiri na biyu, wadanda gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta dauki nauyin su.
Post a Comment
0Comments