Yadda hazikin matashi dan asalin jihar Borno Aji Bukar Bayaro, ya kerawa shahararran dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa MON babban filin wasa na Super Eagle.
Idan baku manta ba, a kwanakin baya na kawo muku hotunan yadda fasihin matashin ya kera kayataccen Masallaci da Jirgin Sama, Gidaje, Motoci, Plaza Da Sauran Abubuwan Ban Mamaki, kamar yadda zaku gani a cikin wa 'yan nan hotunan.
A yanzu haka matashin yakai shekaru biyu da kammala karatun Sakandiri amma saboda rashin wadata ko WAEC da NECO ta gareshi, kasancewarshi maraya iyayanshi duk sun rasu.
Yanzu haka matashin yana zaune a anguwan Dala Fatima Kurti cikin birnin Maidaguri, ga duk mai bukatan taimaka mishi ko daukar nauyin karatunshi zai iya tuntubar matashin kai tsaye ta lambar wayarshi 08132395870.
Irin wannan matasan da Gwamnati tana taimaka musu da irin cigaba da abubuwan da zasu dinga kawowa a kasarmu sai ya bawa mutane mamaki
YANCI HAUSA
Post a Comment
0Comments