Rashin tsaro a Najeriya kirkirarren lamari ne daga yan siyasa - Burtai
Tsohon hafsan hafsoshin Najeriya, Laftanar janar Tukur Burtai ya ce, wannan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya ya samo asali ne, daga yan siyasa.
Tukur ya bayyana haka ne, a wajen wani taro mai taken( Zaman lafiya a Kasata Najeriya,) wanda a gabatar na tsofin dalibai na jami’ar Ibadan, a ranar Juma’a.
Hakazalika burtai ya caccaki mutanen da a tshuwar gwamnatin Buhari suke sukkarsa akan rashin samar da tsaro a Najeriya.
Burtai ya ce, babban abinda ya haifar da rashin tsaro a Najeriya yana da alaka da son rai da son zuciya na wasu dedekun yan siyasa. Inji shi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
Post a Comment
0Comments