ABIN A YABA: A'isha Humaira Ta Raba Tallafin Kuɗi Domin Ragewa Al'umma Raɗaɗin Matsin Rayuwa - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 ABIN A YABA: A'isha Humaira Ta Raba Tallafin Kuɗi Domin Ragewa Al'umma Raɗaɗin Matsin Rayuwa 


Kamar yadda ta saba tallafawa marayu, gajiyayyu, da masu ƙaramin ƙarfi cikin al'umma da sutura, dafaffen abinci da wanda ba dafaffe ba gami da biyawa ɗaurarru masu ƙaramin laifi bashi da kuɗin tara, fitacciyar jaruma a masana'antar Kannywood, Ayshatul humairah, ta raba tallafin kuɗi domin ragewa al'umma raɗaɗin matsin rayuwa da ake ciki a wannan lokaci.


Wannan tallafi kaitsaye ya shiga hannun mutanen da suka cancanta inda aka bi kan tituna aka rabawa waɗanda aka fahimci suna cikin matsi da waɗanda aka fahimci suna da ƙarancin jari a inda suke gudanar da sana'a ko kasuwancinsu. Wasu ta tallafa musu da Naira 20,000, wasu 10,000, wasu 5,000.


A'isha Humaira ta saba gudanar da ire-iren waɗannan ayyuka na jin ƙai da kyautata rayuwar al'umma a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso batare da gajiyawa ba.


Wane fata zaku yi mata?


Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!