A ƙoƙarinsa na samar da ingantaccen ilimi ga yaya mata tare da inganta harkokin kiwon lafiya a Jihar Kano mai girma gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ɗauki gaɓaren kammala aikin gina makarantar koyon aikin Ungurzoma da ke garin Gezawa.
Ita dai wannan makaranta an aza harsashin gininta ne tun lokacin mulkin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi kuma tsohon gwamna Ganduje yayi watsi da ginin nata.
Tun a kwanakin baya ne dai mai girma gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da kwace kwangilar gina wannan makaranta tare da damƙa aikin a hannun sabon dan kwangila wanda zai iya kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci.
A yanzu haka dai ana cigaba da aikin wannan makaranta wacce idan an kammala ake sa ran ɗaliban Jihar Kano za su na samun gurbin karatu domin koyon aikin Ungurzoma wanda hakan zai bunƙasa harkokin kiwon lafiya a
Jihar.
YANCI HAUSA NEWS
Post a Comment
0Comments