SAMA DA MATASA 3,000 NE SUKA HALACI TARON YAN CRYPTO A JIHAR KANO - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 SAMA DA MATASA 3,000 NE SUKA HALACI TARON YAN CRYPTO A JIHAR KANO.










A yammacin jiya ne Dakin Taron Dake Ado Bayero Mall yayi babbar cikar da bai taba yi ba kuma duk da haka mutanen dake waje sun ninka na ciki basu sami damar shiga harabar wajen ba.


Taro ne akai na sada zumunta na masu hada hadar Crypto inda maza da mata masu ciki da masu goyo suka hallaci taron domi kara samun wayar dakai akan yadda zata cigaba da fashewa.


Matasan Wanda ake musu Lakabi da Yan Baiwa sunce bamu shiga gonar kowa ba don haka bazamu kyale wasu suna shiga namu gonakin ba suna yimana yadda suke so, a kwanakin baya da harka tayi karfi lokacin shari oin zabe matasa maida hankali sukai kan mining har aka gama babu abunda ya faru, to gunga de kowa abunyi yake nema.


Wata matashiya data zo daga garin Zaria tace da mining nake biyawa yayana makaranta kuma dole mu maida hankali wajen sake zakulo damar maki.


Muhd King Cash, da Rabiu Biyora, nadaga cikin manyan Jagororin taron sun godewa mahallata taron duk da cewa abunda sukai tsammani ya wuce tunaninsu don haka suna fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.


AN GAISHI KU YAN BAIWA.

Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!