Shin wanene Dakta Bello Habib Galadanchi (Dan Bello)?
A takaice, an haifi Dakta Bello Habib Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello a State College, Pennsylvania, kasar Amurka, ranar 12 ga watan Disamba, na shekarar 1987. Iyayensa sune Habib da Halisa Galadanchi, ‘yan jihar Kano. Bayan haihuwarsa, ya shafe wasu shekaru tare da iyalansa, a babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja, a inda anan ne yayi karatu tare da ‘yan uwansa.
Tsawon lokacin da ya dauka a Najeriya, Dan Bello yayi ayukka daban-daban. Yayi aikin sayar da abinci a bakin hanya, yayi aikin kere-kere, yayi aiki tare da mahaifinsa, a inda ya taimaka masa wurin gudanar da sana’arsa ta sha’anin kiwon lafiya. Sannan yayi aikin kera takalmi yana sayarwa.
Bayan kammala karatunsa na makaranrar Sakandare a shekarar 2006, iyayensa suka karfafa masa gwiwa, suka taimaka masa yaci gaba da karatunsa a kasar Amurka, inda ya samu halartar Pennsylvania State University. Saboda hazakarsa, Dan Bello ya kammala karatunsa na jami’ah a shekarar 2009, kuma ya kammala karatunsa da digiri har guda biyu, da kuma wasu satifiket na daban su ma har guda biyu, saboda hazakarsa da iliminsa da kwakwalwarsa.
A takaice, Dan Bello yayi harkokin fina-finan turanci a baya, kuma yayi aikin jarida, inda ya kasance dan jarida mai kwazo, mai ilimin binciko gaskiya. Yayi aiki da sashen hausa na muryar Amurka, da kuma BBC hausa.
Yayi digirinsa na uku a kasar China, yayi ayukka da dama, kuma a halin yanzu yana koyarwa ne a wata makaranta a kasar China.
Kuma Dan Bello shi dan kasa biyu ne, wato kasar Amurka da kuma Najeriya.
Dan Bello ya samu kyaututtuka na girmamawa masu tarin yawa.
Tun tashin sa, Dan Bello mutum ne mai son yaga an tsayar da gaskiya da adalci a cikin al’ummah. Kuma kullun yana cikin damuwa akan irin yadda yake ganin ana zaluntar ‘yan kasar sa Najeriya. Kuma ya ga yadda sanadiyyar irin wannan zalunci da cin hanci da rashawa da suka yi muna katutu, ana ta jefa al’ummah cikin damuwa da rashin tabbas. Damuwar da take jefa matasan mu cikin wasu harkoki da basu dace ba marasa kyawo, kuma masu hadarin gaske.
Cin hanci da rashawa ya jawo muna rikicin Boko Haram a arewa, ya jawo muna rikicin manoma da makiyaya, wanda sanadiyyar haka muka samu kawunan mu cikin ta’addancin barayin daji.
Saboda dagulewar al’amurra a kasar mu Najeriya, yau an wayi gari, abinci ma ya gagari talakawa!
Dukiyar da ya kamata ayi wa bayin Allah, talakawa aiki da ita, sai a wayi gari wasu ‘yan tsiraru, marasa kishin kasa da al’ummominsu suna kwashewa.
Wannan yasa Dan Bello ya yanke shawara, ya tsunduma cikin bayar da gudummawar sa domin ceto wannan al’ummah da wannan kasa ta mu Najeriya.
Mutane suna ta maganganu da cece-kuce akan bincike da dan Bello yake yi, kuma ya bayyanawa al’ummah. To mu a gaskiya ra’ayin mu akan Dan Bello shine, abun da yake yi yayi kyau. Kawai abunda bamu yarda da shi ba shine, yiwa mutane sharri, wanda mun san da ikon Allah Dan Bello ba zai yi haka ba. Ya zama wajibi Dan Bello ya tabbata yana bincike mai zurfi, domin ya zamo cewa ba kage da sharri zai yiwa mutane ba.
Amma idan gaskiya ya binciko, to muna tare dashi dari-bisa-dari, yaci gaba da bayyanawa al’ummah, domin a ware kuma a banbance tsakanin ‘yan kasa nagari da mugaye, maciya amana, masu ruguza kasa.
Ba ya halatta a bar mugu cikin al’ummah, yana lalata kasa da ‘yan kasa, ba tare da an bayyana shi ba. Kuma yin shiru akan barna da mabarnata babban bala’i ne a kasa, kuma sharri ne a cikin kowace al’ummah.
Irin wannan yin shirun da wasu suke so ayi, shine ya kai mu cikin wannan mummunan hali da muka samu kan mu a ciki yau.
Abun mamaki ne matuka, wai ka ga malamin addini yana sukar Dan Bello. Domin irin wannan aiki na bayyana gaskiya fa aiki ne na malamai. Don haka Kenan Dan Bello aiki yake rage wa malamai. Kuma Malamai ai magada Annabawa ne.
Kuma mun san irin gwagwarmaya da karafkiyar da Annabawa da Manzannin Allah suka yi wurin yaki da zalunci da azzalumai, wurin rusa barna da mabarnata. Wani Annabin an kore shi daga garinsa akan wannan aiki. Wani an daure shi, wani an kashe shi. Babu wani Annabi ko Manzo da bai sha irin wannan dauki ba dadi da mutane ba.
Sahabban Annabi (SAW), su ma mun san irin fama da suka sha.
Kai hatta malamai magabata, irin su Imamu Abu Hanifah, Imamu Malik, Imamu Shafi’i, Imamu Ahmad Bin Hanbali, da sauran malamai, irin su Shaikhul Islamu Ibn Taimiyyah, duk mun ga irin yadda suka sha dauri da duka, da cin mutunci, da tsangwama iri-iri daga wurin azzaluman shugabanni, marasa kishi, masu neman kassara al’ummah.
Kai Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah ma shi a gidan yari Allah yayi masa rasuwa. Sam, duk basu yarda sun mika wuya ga zalunci da azzalumai ba.
Irin abubuwan da ake yi a kasar nan tamu Najeriya, wallahi ba zai taba yiwuwa ace ayi shiru akan sa ba.
Kuma boye gaskiya idan mutum ya san ta, haramun ne a Musulunci. Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“Kuma kada ku lullube gaskiya da karya, kuma ku boye gaskiya, alhali kuwa kuna sane.” [Suratul Bakara, 42]
Kuma Allah yace:
“… Kuma wanene mafi zalunci daga wanda ya boye wata shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa.” [Suratul Bakara, 140]
Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“Wadanda muka bai wa littafi, suna sanin sa kamar yadda suke sanin ‘ya ‘yansu. Kuma lallai wani bangare daga cikin su, hakika, suna boye gaskiya alhali kuwa suna sane.” [Suratul Bakara, 146]
Kuma Allah Madaukaki yace:
“Lallai wadanda suke boye abun da Allah ya saukar na daga gaskiya da hujjoji bayyanannu, da shiriya, bayan mun bayyana su ga mutane a cikin littafi, to wadannan Allah yana tsine masu kuma yana la’antar su, kuma duk masu la’anta suna la’antar su. Sai fa wadanda suka tuba daga cikin su, kuma suka gyara kuskuren su, kuma suka bayyana gaskiyar, to wadannan ina karbar tubansu, kuma ni mai karbar tuba ne, mai jinkai.” [Suratul Bakara, 159-160]
Sannan Allah yana cewa:
“Lallai wadannan da suke boye abun da Allah ya saukar na gaskiya a cikin littafi, kuma suna neman ‘yan kudi kadan da shi, wadannan su sani, ba komai suke ci a cikinsu ba illa wuta, kuma Allah ba zai yi magana da su ba a ranar alkiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi.” [Suratul Bakara, 174]
Kuma Allah yana cewa:
“…Kuma kada ku boye shaida, duk wanda ya boye wata shaida da ya sani, to shi mai zunubi ne. Kuma Allah game da abun da kuke aikatawa masani ne.” [Suratul Bakara, 283]
Kuma Allah yace:
“Ya ku ma’abota littafi! Saboda me kuke lullube gaskiya da karya, kuma kuke boye gaskiya, alhali kuwa kuna sane.” [Suratu Ali Imran, 71]
Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“Kuma ku tuna lokacin da Allah ya riki alkawari da wadanda aka bai wa littafi, “cewa lallai zasu bayyana shi ga mutane, kuma ba zasu boye shi ba.” Sai suka yi jifa da shi a bayan su, kuma suka sayar da shi da ‘yan kudi kadan. Tir da wannan abun da suke saye.” [Suratu Ali Imran, 187]
Kuma Allah yana cewa:
“…Kuma bamu zamanto masu boye shaidar Allah ba. Lallai idan mun yi haka, hakika, muna daga cikin masu zunubi.” [Suratul Ma’idah, 106]
Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“Kuma basu girmama Allah akan hakikanin girmama shi ba, a lokacin da suka ce: “Allah bai saukar da komai ba ga wani mutum.” Kace: “Wanene ya saukar da littafin da Musa yazo da shi, yana haske kuma shiriya ga mutane, wanda kuke sanya shi takardu, kuna bayyana su ga mutane, amma kuma kuna boye mafi yawa daga cikin su, kuma an sanar da ku abunda baku sani ba, da ku da iyayenku?” Kace Allah ne. Ka bar su cikin sharholiyar su suna wasa.” [Suratul An’am, 91]
Kuma Hadisi ya tabbata daga Abi Hurairah, Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah (SAW) yace:
“Duk wanda aka tambaye shi wani ilimi, ko kuma yasan wani ilimi wanda zai amfani al’ummah, wanda kuma boye shi zai zama sanadiyyar cutar da al’ummah, kuma ya boye shi, yaki ya bayyana shi, to za’a sanya masa mari ko sasari da sasarin wutar jahannama a ranar alkiyama.” [Abu Dawuda da Tirmizi ne suka ruwaito shi]
Kuma an karbo daga Abu Sa’id Al-Khudri (RA) yace:
“Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Duk wanda yaga wani abin ki daga cikin ku, to ya gusar dashi da hannunsa, idan bashi da iko, to ya gusar dashi da harshensa, idan bashi da iko, to yaki abin a cikin zuciyarsa, amma kuma fa wannan shine mafi raunin imani.” [Muslim]
Sannan Allah Ya tsarkake kansa daga zalunci, kuma Ya sanya shi abin haramtawa a tsakanin bayi, inda Yace:
“Ya ku bayina! Lallai ne Ni, Na haramta zalunci wa kaina, kuma Na sanya shi abin haramtawa a tsakaninku, don haka kada ku zalunci juna.” [Musulim ya ruwaito shi]
Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya wajabta wa al’ummarsa su taimaki wanda aka zalunta, wato su kwato masa hakkin sa wurin wanda ya zalunce shi, sannan kuma su taimaki azzalumi, wato su hana shi aikata zaluncin. Annabi Muhammad (SAW) yace:
“Ka taimaki Dan uwanka, shine azzalumi ko shine wanda aka zalunta. Sai sahabbai suka ce ya Annabin Allah, mun san yadda za mu taimaki wanda aka zalunta, wato mu kwato masa hakkin sa. To shi azzalumi ta yaya zamu taimake shi? Sai Annabi Muhammad (SAW) yace, ku hana shi aikata zaluncin, shine taimakon da zaku yi masa.”
Kuma Manzon Allah (SAW) Yace:
“Zalunci duhu ne ranar alkiyama.”
Irin wadannan nassoshi suna nan masu tarin yawa!
Sannan yanzu don Allah ku kalli irin wariya da nuna banbanci da ake nunawa yankin arewa. An ware wasu irin makudan kudade, na fitar hankali, domin a gina wata hanya a kudancin kasar nan. Dubi wannan irin nuna babbanci da muke gani, kuma da ‘yan uwanmu ‘yan arewa ake shirya irin wannan danyen aiki.
Sannan za’a gida wasu gidaje, karkashin wani shiri mai suna, Renewed Hope City Scheme. Kowa yasan Shugaba Tinubu bai ci zabe a jihar Lagos ba, ya samu kuri’u masu dama a yankin arewa, amma jihar Lagos kawai, a karkashin wannan shiri, zata samu gidaje sama da unit dubu biyu. A daya bangaren kuma, dukkanin jihohi bakwai na arewa-maso-yamma, baki dayansu, zasu samu unit dari biyar kawai.
Sannan idan mun zo akan maganar wutar lantarki, wallahi arewa baki daya bamu da wutar lantarki, amma don girman Allah kazo nan kudancin kasar nan ka ga ikon Allah. Mu arewa sai kace ba ‘yan kasa ba. Babu inda bana shiga a kudancin kasar nan.
Wutar lantarki a yankin kudu ga ta nan a ko’ina. Amma a arewa an bar mu haka nan babu wuta.
Talakawan mu da matasan mu masu gudanar da sana’o’i da wutar lantarki duk an bar su a cikin rashin tabbas.
Akwai yankin arewa da tun azumin Ramadan wallahi basu da wutar lantarki.
Kuma wai duk a haka so ake yi muyi shiru, kar muyi magana.
To mu a fahimtar mu yin shiru akan barna haramun ne. Kuma boye gaskiya shi ma haramun ne. Kuma Allah zai kama duk mai yin wannan!
Don haka, Dan Bello da ire-irensa su sani, al’ummar mu tana tare da su dari-bisa-dari. Duk wanda zai yi shiru kuma ya rage nashi, sai yayi shiru. Idan mun je gaban Allah, Allah zai bayyana masu gaskiya!
Mu sani, Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bamu labari, zai la’anci duk al’ummar da aka wayi gari wasu suna yin ba daidai ba daga cikinsu, kuma suyi shiru, suki yin magana, ko suki yin wani kokari da yunkurin hana su.
Allah Yace a cikin littafinSa Mai girma:
“An la’ani wadanda suka kafirta daga Bani Isra’ila a kan harshen Dawuda da Isa dan Maryama. Wannan kuwa saboda sabon Allah (wato zunubi), da barna da suke yi. Sun kasance suna ta’adi (suna ketare iyaka), kuma sun kasance ba sa hana juna aikata mummunan aikin, wanda suka aikata. Hakika, abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.” [Suratul Ma’idah, 78-79]
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau
Post a Comment
0Comments