Tinubu ya amince da wani sabon tsarin riƙe kwararrun Likitoci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya amince da wata sabuwar manufa ta ƙasa da ke neman magance karuwar Ma'aikatan kiwon lafiya masu guduwa zuwa kasashen waje domin yin aiki.
An bayyana hakan ne a wata Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ministan Lafiya da jin dadin jama’a Ali Pate a ranar Litinin.
Ministan ya ce manufar wata dabara ce da za ta sarrafa gami da magance hijirar da Ma’aikatan Lafiya ke yi zuwa ƙasashen ƙetare.
Ya ƙara da cewa Manufar za ta kuma karfafa komawar kwararrun Likitoci zuwa Najeriya ta hanyar karfafa musu gwiwa tare da basu alawus-alawus domin mayar da su cikin tsarin kiwon Lafiyar ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wannan tsarin zai yi ƙoƙarin dawo da kwararrun mutanen da ke ƙasashen waje don cike gibin da ke cikin ɓangaren kiwon lafiya.
Haka kuma manufofin sun kulla yarjejeniya da sauran kasashen waje don tabbatar da cewa musayar Ma'aikatan lafiya ta amfanar da Najeriya.
“Wadannan yarjejeniyoyin biyu da na bangarori daban-daban an tsara su ne don kare muradun kasa tare da mutunta hakki da buri na kwararru a fannin kiwon lafiya.
Muna kira ga kasashen da suka karɓi Ma'aikaci da su aiwatar da tsarin "1:1" wato su horar mana da Ma'aikaci ɗaya don maye gurbin kowane Ma'aikacin Najeriya da suke son ɗauka wanda ya samu horo a Najeriya.
Ministan ya ce manufar ta yarda da mahimmancin daidaiton rayuwar aiki kuma ta haɗa da wani tanadi don kula da lafiyar kwakwalwa na yau da kullun, da kuma lokutan aiki masu dacewa musamman ga Matasan Likitoci.
"Wadannan matakan suna nufin samar da yanayin aiki mai kyau, da haɓaka gamsuwar yanayin gudanar da aiki," in ji Pate.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Post a Comment
0Comments