Yadda El-Rufai Ya Je Gidan Atiku Neman Aure - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 Yadda El-Rufai Ya Je Gidan Atiku Neman Aure







A Yau Laraba ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karbi bakuncin tawagar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai a Gidansa dake Asokoro dake Abuja.


A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman (Broadcast Media) ga tsohon mataimakin shugaban kasar AbdulRasheed Shehu ya fitar, ya ce sun kai ziyarar ne domin neman auren diyar Atiku, Hafsat Atiku Abubakar a hukumance da iyalan Kashim Imam..


Taron dai ya samu halartar manyan baki da suka haÉ—a da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da tsaffin Gwamnoni Sule Lamido na jihar Jigawa da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da dai sauransu.


Sanarwar da Shehu ta wallafa a kan X tare da hotunan tana cewa: “Mai girma Atiku Abubakar ya yi maraba da iyalan Kashim Imam, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, zuwa gidansa na Asokoro. Tawagar ta zo ne domin neman auren diyar sa, Hafsat Atiku Abubakar.


Daga: YANCI HAUSA NEWS 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!