An rufe jami'ar Maiduguri da ke Jihar Borno har zuwa wani lokaci sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye sassan babban birnin Jihar.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta sanar da rufe jami’ar a wata Sanarwa da magatakardar ta Ahmad A Lawan ya fitar a ranar Talata, inda ya jajantawa ma’aikata da daliban da Iftila'in ya shafa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wannan yana sanar da É—aukacin Ma’aikata da É—alibai cewa, bisa la’akari da mummunan Iftila'in ambaliyar ruwa da ya faru a Maiduguri, hukumar jami’ar ta dakatar da duk wasu laccoci a jami’ar tare da rufe ofisoshi na wani dan lokaci har sai abin ya daidaita.
Hukumomi suna É—aukar matakai don kare ma'aikata da É—alibai da kuma tantance yanayin da ake ciki kafin a É—auki wasu matakan da suka dace nan gaba.
Hukumar Jami'ar ta jajantawa É—aukacin ma’aikata da daliban da Iftila'in ambaliyar ruwa ya shafa, tare da addu’ar Allah ya kiyaye sake faruwar lamarin nan gaba”.
Ambaliyar dai na da nasaba da rugujewar madatsar ruwa ta Alau da ake zargin ta cika tsawon mako guda.
Dimokuradiyya TV ta ruwaito yadda dubban mazauna garin suka fice daga gidajensu sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan babban birnin Maiduguri.
Lokaci na karshe da dam din ya samu irin wannan matsala shi ne a shekarar 1994 wanda ya haifar da ambaliya da ba a taba gani ba a Maiduguri, inda kusan rabin garin ya cika da ruwa.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Post a Comment
0Comments