Har yanzu harajin VAT yana nan a 7.5% a Najeriya – Ministan Kudi Edun

YANCI HAUSA
By -
0

 Har yanzu harajin VAT yana nan a 7.5% a Najeriya – Ministan Kudi Edun



Ministan Kudi na Najeriya Wale Edun a ranar Litinin ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Gwamnati ta ƙara harajin VAT zuwa kashi 10 cikin 100, saɓanin yadda yake a baya kashi 7.5 cikin 100.


Edun ya bayyana haka ne a cikin wata Sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin, inda ya tabbatar da cewa adadin harajin na VAT yana nan kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin harajin da ke tattare da kayayyaki da ayyuka wato kashi 7.5 cikin dari.


A cewarsa abin da Gwamnati ta mayar da hankali a kai shi ne bullo da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar ƴan Nijeriya ba wai ƙara talauta ƴan ƙasa ba.


Ya jaddada cewa, wannan ne ya sa a kwanan nan Gwamnati ta ɓullo da shirin cire harajin shigo da kayan masarufi na kwanaki 150 da shigo da sauran kayan amfanin yau da kullun kamar shinkafa alkama da sauransu.


"Adadin harajin VAT a halin yanzu yana nan kashi 7.5 bisa 100, kuma wannan shi ne abin da Gwamnati ke karba a kan dukkanin nau’ukan kayayyakin da ake cinikayyarsu, don haka Gwamnatin tarayya ko wata hukuma ba za ta yi wani abu da ya sabawa abinda waɗannan dokokin suka gindaya ba", inji shi.


Daga YANCI HAUSA NEWS 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!