Bayan kama Ajaero, Jami'an DSS sun kewaye Ofishin SERAP da ke Abuja
Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun mamaye Ofishin Æ™ungiyar kare hakkin bil'adama da kula da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da jami'an DSS ɗin suka kama Joe Ajaero Shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC.
Cikakkun bayanai game da mamayar Ofishin SERAP da DSS tayi har yanzu bai bayyana ba, amma a cewar wata Sanarwa da Æ™ungiyar ta wallafa ta dandalin X, sashen da ke kula da shari'a na kungiyar ya bayyana cewa jami’an sun buÆ™aci ganin shugaban kungiyar ne.
Yace Jami’an hukumar ta DSS sun mamaye Ofishin Æ™ungiyar su da ke Abuja ba bisa ka’ida ba suna neman ganin daraktan mu.
"Dole ne Shugaba Tinubu ya umarci hukumar DSS da ta gaggauta kawo karshen cin zarafin da Jami'an hukumar ke yiwa Æ´an Najeriya” inji Sanarwar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne SERAP ta ba wa Shugaba Tinubu wa'adin kwanaki 48 don ya sauya karin farashin da aka yiwa Man Fetur a ƙasar nan.
Ta roki Shugaban Æ™asar da ya yi amfani da “matsayin Mulkin sa wajen umurtar kamfanin Man Fetur na Æ™asa (NNPCL) da ya gaggauta sauya karin farashin Man Fetur da ake zargin an yi ba bisa ka’ida ba.
A cikin budaddiyar wasika mai ɗauke da kwanan watan 7 ga watan Satumban 2024, mai ɗauke da sa hannun Mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce "Karin farashin Man Fetur ya zama wani babban cin zarafi ga tsarin Mulki da kuma hakkin dan Adam na ƙasa da ƙasa."
Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Post a Comment
0Comments