Kar ku karaya akan Najeriya – Atiku ga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje

YANCI HAUSA
By -
0

 Kar ku karaya akan Najeriya – Atiku ga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje



Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya shawarci ƴan Najeriya mazauna kasashen waje da su ci gaba da jajircewa tare da kyautata zaton samun makoma mai kyau ga Najeriya.


Ya yi wannan kiran ne yayin wani taron tattaunawa da wasu ƴan Najeriya mazauna kasashen waje a ranar Asabar.


Atiku ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa a kan al’ummar kasar duk da kalubalen da tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.


A cewarsa halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ya janyo wa miliyoyin ƴan Najeriya wahalhalun da ba za a iya mantawa da su ba, kuma ana ci gaba da samun ƙaruwar alkaluman talauci.


Ya ce ƴan Najeriya mazauna kasashen waje suna taka rawar gani wajen tsara makomar ƙasar mai kyau.


Ina roƙon ku da kada ku yi kasala, har yanzu ƙarfinku da juriyarku na da mahimmanci ga makomar Najeriya.


A matsayinku na ƴan Najeriya mazauna kasashen waje kuna da masaniya ta musamman kan yadda Shugabanci nagari da tafiyar da tattalin arziki yake kasancewa a ƙasashen da ku ke.


Ina ƙarfafa ku da ku ci gaba da yin addu'a don kubutar da Nijeriya daga halin da take ciki.


Addu'o'in ku da goyon bayanku na iya taimakawa wajen kawo sauyin da muke buƙata.


"Na yi imani da tasirin ƙasarmu mai girma, kuma na san cewa tare da haɗin gwiwa za mu iya shawo kan kalubalen da muke fuskanta tare da gina Najeriya mai kyau ga kowa da kowa," in ji shi.


Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma ƙara karfafa gwiwar ƴan Najeriya da su ci gaba da tallafa wa iyalansu da abokansu a gida.


Daga YANCI HAUSA NEWS 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!