Mahaifiya tamkar lokaci take - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 ðŸ’™ðŸ’™❤️ADDINI NASIHA NE ❤️💙💙



MAHAIFIYA 


Mahaifiya tamkar lokaci take.. Idan ta wuce bata maimaituwa.. (wato idan ka rasata babu mai cike maka gurbinta, sai anyi da gaske ka samu Mai kyatata maka Amma dae ba xa'a Kai tamkar uwah ba Domin kama da wane bata wane) 


Mahaifiya ita ce tubalin farko na ginin rayuqar kowanne mutum.. Ita ce malamarka ta farko, kuma ita ce ta samar maka da abincinka na farko.. Duk wani mai kaunarka to bai kai koda kusa da ita ba. 


- MAHAIFIYA tafi kowanne mahaluki jin tausayinka.. Duk kudinka duk mulkinka duk tsufanka, in dai mahaifiyarka tana nan araye, to tausayinka take ji.. Rarrashinka takeyi.. Bata son duk abinda zai tada ma hankali. 


Mahaifiya tafi kowa guje wa faruwar duk abinda zai tashi hankalinka.. Tafi dukkan mutane kokarin samar maka da mafita alokacin daka shiga matsala. 


Zata iya hakura da yunwa domin ta ciyar dakai. Zata iya zama cikin tsaraici domin ta tufatar dakai. Zata iya shiga kowacce matsala domin tabbatar da cewa kai ka zauna lafiya. Zata iya hakura da jin dadin duniya domin sanyaka farin ciki. 


Ya Allah ka sanya iyayenmu Maza da Mata a karkaashin inuwarka aranar Alkiyamah. Kuma ka sanyasu cikin bayinka wadanda zaka shigar dasu aljannarka ba tare da hisabi ba. Ameen. 


Wannan sadaukarwa ce ga wacce ita ce sanadiyyar alkhairai gareni arayuwata baki daya.Addu'a ta Allah ubangiji ka gafartawa Duk wata mai Amsa sunan uwah, Fatana Allah ya kyautata makomar iyayenmu ya hadamu dasu a Aljanna alfarmar annabiï·º. Ameen.

Barka da Safiya


Rabiu Suraj Bageewar

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!