Matatar Dangote za ta fara rarraba Man Fetur a ranar Lahadi - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 Matatar Dangote za ta fara rarraba Man Fetur a ranar Lahadi - FG



Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki Mista Wale Edun ya ce Matatar Man Dangote za ta fara rarraba tataccen Man Fetur a ranar Lahadi 15 ga watan Satumban 2024.


Edun wanda ya samu wakilcin Shugaban Hukumar tara haraji ta Tarayya (FIRS) Dakta Zacch Adedeji ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a.


"Ina mai farin cikin sanar da cewa an kammala dukkan yarjejeniyar, kuma za a fara dakon kashin farko na Man Fetur daga Matatar Dangote a ranar Lahadi 15 ga Satumba.


Daga ranar 1 ga Oktoba, kamfanin NNPC zai fara samar da kusan ganga 385 na danyen mai ga Matatar Dangote wanda kuma za a biya da Naira.


"Matatar Dangote za ta siyar da Man Diesel a Naira ga duk mai buƙata. A halin yanzu kuma NNPC ce kadai za a sayar wa Man Fetur daga Matatar, yayin da ita kuma NNPC za ta siyarwa ƴan kasuwa daban-daban".


Edun ya tuna cewa Majalisar zartaswa ta Tarayya (FEC) a karkashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Tinubu ta amince da sayar da danyen mai ga Matatun gida a Naira da kuma siyan Man Fetur duk a Naira.


Ya ce shirin zai taimaka wajen rage matsin lambar da ake yi wa Naira, da kawar da kashe-kashen hada-hadar kasuwanci da kuma inganta samar da Man Fetur a ƙasar.


Ministan ya ce kwamitin aiwatarwa da shi da sauran kwamitocin sun yi aiki tukuru tare da kamfanin Man Fetur na NNPC da Dangote wajen tsara bayanan hanyoyin aiwatar da amincewar FEC.


Edun ya jagoranci kwamitin Shugaban ƙasa na tabbatar da an siyar da ɗanyen Mai, da wanda aka tace da ake amfani da shi a cikin gida a Naira.


Daga YANCI HAUSA NEWS 

Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!