Sarki Charles ya karɓi baƙuncin Tinubu a fadar Buckingham
Shugaba Bola Tinubu ya samu kyakkyawar tarba ranar Laraba a Birnin Landan daga mai martaba Sarki Charles na Uku a fadar Buckingham, inda suka yi wata ganawar sirri da ke nuna kyakyawar alaƙa tsakanin Najeriya da Burtaniya.
Wannan shi ne karo na farko da Shugabannin biyu za su gana tun bayan da suka haÉ—u a Dubai a taron COP 28 a taron sauyin yanayi a bara.
A cewar mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga, ganawar ta kasance bisa buƙatar Sarkin.
Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi duniya da shiyya-shiyya, tare da mai da hankali kan ƙalubalen da canjin yanayi ke haifarwa.
Shugaba Tinubu da Mai Martaba sun kuma duba damar yin haÉ—in gwiwa tare da sa ran taron COP 29 na nan gaba da za a yi a Azerbaijan da kuma taron shugabannin Kasashen Commonwealth (CHOGM) dangane da Samoa za su kasance cikin nasara.
Shugaba Tinubu ya nanata kudurin Najeriya na ganin an magance sauyin yanayi ta hanyar da ta dace da manufofin tsaron makamashin kasar, yayin da ya tabbatar da a shirye Najeriya take ta rungumi dabarun duniya don samun cigaba mai É—orewa.
A yayin tattaunawar tasu shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan sabbin hanyoyin da za a bi don samar da kuÉ—aÉ—e ga matsalar sauyin yanayi tare da bayyana muradun su wajen karfafa haÉ—in gwiwa ta hanyar yin amfani da matsayin Najeriya a Afirka da Commonwealth.
Daga YANCI HAUSA NEWS
Post a Comment
0Comments