Dan Allah Ai Sharing Allah Yasa muyi Tarayya a Ladan Aikin.
DON ALLAH MU KARANTA KUMA MU YI SHARING ZUWA GA SAURAN ƳAN UWA MUSULMAI. SABODA YANZU ABUN YA ZAMA MATSALA TA WANNAN AL'AMMARIN, IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA MAI YIWA WANNAN GAWAR WANKA, KO
KUMA KAGA MALAMIN DA ZAIYI
WANKAN YANA TA MULKI SAI LOKACIN DAYA GA DAMA ZAI ZO YAYI WANKAN.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI.
FALALAR WANKAN GAWA.
Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi
Wanda Manzon Allah (S.A.W)
Yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke
mamaci, kuma ya rufa masa
asiri, Allah Zai gafarta masa sau
arba’in.’’
A wani hadisin kuma Manzon Allah
(S.A.W) Yace, ”Duk wanda ya
wanke mamaci kuma ya rufa masa
asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljanna Kwarra (wato Launin Tufafin).
SHARUÆŠÆŠAN WANKAN GAWA.
Daga cikin sharaÉ—an wankan gawa
sune:-
1. Ana buƙatar waɗanda zasu wanke
mamacin su zamanto makusantan sa (misali, Iyaye, ƙanne, yayye, ko ƴaƴa, da sauransu).
2. Ana buƙatar maza su jiɓinci wanke maza, suma mata su jiɓinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa hakama Mace zata iya wanke Mijinta).
3. Ba sharaÉ—i bane lallai sai anyi
amfani da ruwan zafi ba.
YADDA AKE YIN WANKAN GAWA
Ana yin wankan gawa mara-mara ne
(misali, Sau Uku(3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9)).
Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a cikin hadisin Ummu Adiya(R.A).
WaÉ—anda zasu yi wa mamaci wanka su zasu yi la’akari suga wanka nawa ya dace suyi masa.
Da farko dai kafin a fara wankan
akwai abubuwa guda Uku(3) da za’a fara yi wa mamacin. Su ne kamar haka:-
1. Za’a cire masa suturar da take
jikinsa, amma za’a sami É—an kyalle a rufe masa al’aurarsa.
2. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na É“angaren mafita biyu wato (Bawali da Gayadi).
3. Idan macace, za’a tsefe kitsan dake kanta, a wanke kan, sannan ayi LallaÉ“i uku a kan ( wato Kalba guda Uku). Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.
Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba É—aya.
YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun
zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun gama abubuwan
da suke sama sai su fara wankan. Da farko dai zasu tanadi ruwa
kashi Uku (3), kowanne ruwa za ayi wanka É—aya ne da shi.
WANKAN FARKO (RUWAN FARKO)
Wannan wankan za ayi wa mamaci ne wanka irin Wankan Janaba.
Da farko za’a fara yiwa mamaci alwala ne, kamar irin alwalar Sallah, saidai wajen kuskurar baki da shaÆ™ar hanci za’a shafa masa ruwa ne kawai a bakin tare da hancin.
Bayan anyi masa alwala, sai kuma a
zuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu.
WANKA NA BIYU (RUWA NA BIYU KENAN).
Bayan anyi masa wanka na sama
wato na Janaba, sai kuma a samu Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin da shi.
Wato za’a samu Soso da Sabulu a
cuÉ—a masa jikinsa sosai (Kamar dai
yadda ake wanka irin na Soso da
Sabulu, saidai za’a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun). Bayan an gama cuÉ—a shi sai a É—auraye Kumfar da wannan ruwan.
WANKA NA UKU (RUWA NA UKU KENAN).
Bayan anyi masa wanka na sama,
wato na Soso da Sabulu, to sai kuma a samu ruwa na ƙarshe wato na Uku a zuba Turare me ƙamshi (Sosai) a ciki, sannan sai a wanke mamacin da shi.
Anfi son ayi amfani da Turaren Kafur,
to amma idan ba’a same shi ba to za’a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai Bayan an gama wankan Turaren, to sai a tsane jikin mamacin a sa masa Likkafani.
YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7), KO TARA (9).
Idan masu yiwa mamaci wanka sun
zaɓi su yi masa wanka biyar(5),ko bakwai(7), ko tara(9), to wanka na biyu(2) wato na Soso da Sabulu shi zasu ta maimaitawa.
Amma dole ne na Janaba shi ne a Farko, sannan na Turare shi ne a karshe.
MISALIN YADDA ZA'AYI WANKAN SAU BIYAR (5).
1. Na farko shi ne na Janaba
2. Na biyu shi ne na Soso da Sabulu
3. Na Uku shi ne na Soso da Sabulu
4. Na Hudu shi ne na Soso da Sabulu.
5. Na Biyar shi ne na Turare.
MA’ASSALAM.
Dan Allah ka/ki daure a jarraba ko da a abin wasan yara ne yadda za a tabbatar da karatun ya zauna.
DA FATAN ZAKA/ZAKI AIKAWA DA
ABOKAN KA/KI WANNAN SAƘO DOMIN SUMA SU ƘARU. Ubangiji Allah yasa zamu dace Amin.
Post a Comment
0Comments