Zaki ya kashe wani ma’aikacin gidan zoo na Obasanjo

YANCI HAUSA
By -
0
Ajali: Zaki ya kashe wani ma’aikacin gidan zoo na Obasanjo
Wani zaki a gidan adana namun daji na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a jihar Ogun ya kashe ma’aikacin gidan mai suna Babaji Daule.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar a babban birnin jihar Ogun.

An tattaro cewa zakin ya afkawa Daule mai shekaru 35 daga jihar Bauchi a gidan dabbobi na OOPL.

Lamarin wanda babban jami’in tsaro na OOPL ya bayar da rahotonsa da misalin karfe 7:40 na safe, an ce ya faru ne a lokacin da mai kula da zakin da ke gidan namun daji “ya yi sakaci da kula da kulle shingen shingen zakin kafin tunkarar kejin don ciyar da dabbar.

“Wannan sakacin ya baiwa zakin damar tserewa tare da kai masa hari, wanda ya yi sanadin raunata wuyan ma’aikacin kuma daga bisani ya mutu.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!