Al'ummar Kaduna Shaida ne akan salon Mulkin APC, tabbas za mu lashe zaɓen LGA - PDP
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta shiga fafata zaɓen ƙananan Hukumomi a Jihar Kaduna duk da fargabar da suka yi na cewa jam'iyyar APC mai Mulki za ta tafka maguɗi a zaɓen.
Dan Takarar Gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 Isah Ashiru ne ya bada wannan tabbacin a ranar Juma’a a wata tattaunawa da yayi da Wakilinmu a Kaduna.
Jam’iyyun da ke Mulki a Najeriya suna yin komai domin danne sakamakon zaɓe a duka zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar a Najeriya, lamarin da ya sa Majalisar dattawa a ranar Alhamis ta bayyana duk zaɓen da aka yi a matsayin abin kunya.
Sai dai Mista Ashiru yana da yakinin jam'iyyarsa ta PDP za ta sauya lamarin a Jihar Kaduna saboda ƙarfi da farin jinin da jam'iyyar take da shi a Jihar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (SIECOM) ta shirya gudanar da zaɓen a ranar 19 ga watan Oktoban shekarar nan da muke ciki.
Gwamna Uba Sani shi ma ya bayyana kwarin guiwar cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe dukkan zaɓen a ƙananan Hukumomi 23 na Jihar.
Daga YANCI HAUSA NEWS
Post a Comment
0Comments