Ƴan bindigã sun harbe ɗan Takarar APC har lahira a Jihar Ogun

YANCI HAUSA
By -
0

 Ƴan bindigã sun harbe ɗan Takarar APC har lahira a Jihar Ogun



Wasu ƴan bindigã da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun harbe Adeleke Adeyinka ɗan Takarar kansila na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Abeokuta ta Kudu a ranar Asabar.


Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na rana a unguwar Jide Jones da ke Oke Ilewo Abeokuta Jihar Ogun


Wakilinmu ya bamu rahoton cewa maharan sun iso ne a wata mota mai baƙin gilashi, inda ɗaya daga cikinsu ya fito ya harbe Adeyinka a harbin kusa da kusa, sannan suka farfasa masa kai har ya mutu.


A cikin wani faifan bidiyo da wakilinmu ya gani, mamacin yana kwance fuskarsa a cikin jinì.


A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta "Kisan ya faru ne da misalin karfe 2 na rana, lamarin da ya ba kowa mamaki, babu wanda ya san ko harin daga ƴan kungiyar asiri ne ko a'a, Al'ummar yankin duk sun rufe shagunansu, al'amarin da haifar da tashin hankali matuƙa".


Mamacin tsohon Shugaban Matasan karamar hukumar Abeokuta ta kudu ne, inda yanzu yake neman kujerar kansila a mazaba ta 15 a zaɓen kananan hukumomin da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.


An ce Adeyinka ma’aikacin kungiyar sufuri ne a unguwar Panseke da ke Abeokuta a lokacin da yake raye.


Daga YANCI HAUSA NEWS 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!