Babu wani shiri na yin maguɗin zaɓen LGA a Kaduna - Shugabar Hukumar zaɓe
Shugabar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) Hajiya Hajara Mohammed ta bayyana cewa babu wani shiri da hukumar ta yi na yin maguɗi a zaben ƙananan hukumomi da ke tafe a Jihar.
Ta kuma ja kunnen ƴan Siyasa da su guji tashin hankali da kalaman ɓatanci a lokacin zaɓe.
Shugabar ta yi wadannan kalamai ne a yayin taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a ranar Asabar, inda ta buƙaci dukkanin jam’iyyun Siyasa da su marawa jami’an da aka tura mazabarsu baya wajen gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ta baiwa al'ummar Jihar Kaduna tabbacin cewa zaɓen zai gudana ne a ranar 19 ga watan Oktoban 2024 kamar yadda hukumar ta sanar.
Ta kuma buƙaci jam’iyyun siyasa da su ɗauki ƙaddarar faduwa da kyakkyawar zuciya tare da yin nuni da cewa za a sake yin wani zaɓen bayan cikar wa'adi.
Daga YANCI HAUSA NEWS
Post a Comment
0Comments