Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shatima, yace dole ne a sauya yanayin rashin aikin yi da ake fuskanta a Najeriya.
Kashim shatima, yayi wannan alkawarin ne a yau asabar, A yayin da yaje wani taron kaddamar da dabarun bunkasa jari a jihar Nasarawa.
Khashim, ya jaddada cewa manufar gwamnatin Nijeriya shine, Ta baiwa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa domin samun kwarewa a fadin duniya.
Ya kara da cewa, Abubuwan dake damun tsarin ilimi a kasarmu, akwai yawan dalibai da malamai, da yawan matasa da basu da aikin yi, Wanda a sakamakon hakan dole ya mayar da al'ummarmu koma baya.
Daga
YANCI HAUSA NEWS
Post a Comment
0Comments