Shaikh Bashir Shaikh Ja'afaru ya jagoranci Mauludin Annabi SAW a gidansa na Katsina

YANCI HAUSA
By -
0

 Shaikh Bashir Shaikh Ja'afaru ya jagoranci Mauludin Annabi SAW a gidansa na Katsina


Shehin Malamin, ya jagoranci bikin Mauludin domin nuna ƙauna ga fíyáyáyyén halittá Annabi SAW, inda ya gudanar da walima da kuma tara malamai don nuna kaɗan daga cikin darajar da Annabi SAW yake da ita.


Daga cikin shawarwarin da malaman suka bada a lokacin bikin Mauludin, sun jaddada cewa halayen Annabi SAW ne ya dace kowanne músúlmì ya bi fiye da komai.







Sun yi nuni da cewa, dárájar Annabi ta wuce yadda kowa yake tunani a zahiri da baɗili, sun ce kamata yayi duk lokaci-lokaci a rinƙa bikin tunawa da ranar haihuwar sa ba dole sai shekara-shekara ba.


Katsina Post ta samu cewa, bikin Mauludin ya gudana a ranar Asabar 12 ga wata Oktoba 2024, inda mutane da dama ne suka ziyarci bikin Mauludin, tare da yin addu'ar Allah Ubangiji ya sa wata shekarar ayi da su.

Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!