YARON TSOHON GWAMNAN JIHAR KADUNA FAISAL YAYI HATSARI YA RASU
Shuaibu Abdullahi
YARON tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmad Makarfi, Faisal Ahmed Mohammed Makarfi, ya rasu.
Wasu na kusa da shi ne suka tabbatar da rasuwar cikin Daren nan.
Rahotan ya ce Faisal ya rasu da yammacin yau Asabar bayan ya gamu da tsari a kan titin Kaduna zuwa Zaria.
Rahotan ya ce sai da aka fara garzayawa da Faisal zuwa Asibiti daga bayan likitoci suka tabbatar an rasa shi.
Zuwa yanzu babu wata cikakkiyar sanarwa daga Iyalin Sanata Makarfi, amma an tafi da gawar zuwa gidan don gudanar da Janaza bisa koyarwar addinin Islama.
Post a Comment
0Comments