An fitar da man jirgin sama na kamfanin matatar Dangote zuwa London, Iceland, da sauran filayen jiragen sama na duniya
Matatar man Dangote ta yi nasarar fitar da man jiragen sama zuwa wasu kasashen duniya da suka hada da filayen jiragen sama na Iceland, Tenerife, da kuma Landan.
Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na SP Global Commodity Insights ya fitar, ya ce man da matatar ta ke samarwa a Najeriya ya kai fitattun wurare kamar filin tashi da saukar jiragen sama na Heathrow da ke Birtaniya, yayin da matatar man ke ci gaba da habaka ayyukanta.
Rahoton ya kara da cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara, an kai akasarin kayayyakin da matatar ta ke samarwa zuwa cibiyar jigilar kayayyaki ta Lome da ke kasar Togo.
Post a Comment
0Comments