HORAR DA MATASA DA MATA DOMIN DOGARO DAKAI DAGA CIBIYAR Barau - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 HORAR DA MATASA DA MATA DOMIN DOGARO DAKAI DAGA CIBIYAR Barau Reporters







Taron Matasa da Mata na Barau kan bunkasa tattalin arziki da dogaro dakai, kungiyar Barau Reporters ta samar da manufa akan yadda matasa da mata zasu sami hanyoyin dogaro dakaia a fadin Jihar Kano muhimman Ilimin kimiya da Fasaha, wanda ake koyarwa da harshen Hausa. 

Shirin na tsawon watanni uku zai mayar da hankali kan haɓaka dogaro dakai da ƙwarewa akan ilimin kimiya da fasaha don taimaka wa mahalarta su gina da haɓaka kasuwancinsu cikin hanyoyi kamar haka:


HAƁAKA ƘWAREWA: Horarwa kan ƙirƙirar kasuwanci ta yanar gizo, talla a kafofin sada zumunta, kasuwanci ta yanar gizo, SEO, sarrafa kasuwar kudaden ketare.


KAYAN AIKI: Mahalarta za su sami damar yin amfani da kayan dijital da aka tsara don su kamar rukunin yanar gizo na VTU da kasuwanci ta yanar gizo.


TAKADDUN SHAIDA DA JAGORANCI: Za a ba wa waɗanda suka kammala shirin takardar shaida, kayan aiki masu amfani, da jagoranci don tallafa musu a harkar kasuwanci.


CANCANTA: A bude shirin yake ga matasa da mata na Jihar Kano masu na'urar Android (samfurin 4.2 ko sama da haka).

BUKATAR SHIRIN: Dole ne mahalarta su halarci dukkan zaman shirin tare da yin hulɗa sosai.

Mun gode

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!