ABIN DA YA SA NA DAWO YIN AKTIN ~ Ahmad Bifa - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 ABIN DA YA SA NA DAWO YIN AKTIN ~ Ahmad Bifa


Daga YANCI HAUSA NEWS 


Fitaccen Furodusa kuma Darakta a Kannywood Ahmad Bifa, ya bayyana dalilin sa hada aiki uku wanda yanzu ya rikide yake fitowa a matsayin Jarumi.




A tattaunawar da YANCI HAUSA NEWS ta yi da Ahmad Bifa ya ce matsalolin da yake fuskanta a wajen aiki da Jarumai ne suka sa ya ga shi ma fa zai iya zama jarumin, don haka kawai ya yanke shawarar bari kawai ya fara don ya magance wasu matsalolin da yake samu idan ya tashi aiki da wasu Jaruman.


"Matsaloli da Jarumai suke yawan bayarwa , wani lokacin sai ka ga Mutum ba kyau ya fi ka ba, ba sura ya fi ka ba, amma da ka kira shi ya yi maka aiki sai ya yi ta ja maka aji.


To wannan dalilin ya sa na fara fitowa a cikin fim din da na shirya mai dogon zango Amaryar Tik Tok saboda kada na fara da wani ya ba ni matsala.


Kuma sai gashi a hankali Alhamdulillah, Jama'a sun fara ganin nima akwai gudummawa da zan iya bayarwa a fagen, har ma aka fara kira na ina fitowa a wasu finafinan ban da nawa."


Ko ya kake kallon ka a matsayin Jarumi a maimakon matsayin ka na Darakta a baya?


"Ai daman idan aka ce ka fara bada umarni ka san ya Jarumi yake da sauran abubuwa, saboda shi mai bada Umarni zai san duk abin da yake tafiya a cikin fim. 


Zama Darakta da kuma zama Jarumi daga baya ya taimaka mini wajen duk wata dama da zan yi amfani da ita wajen aikin bada Umarni.


Kuma wani abu da na lura da shi na ci gaban rayuwa da na samu a yanzu, a baya sai in je wajen taro ma a hana ni shiga, ko a rinka tambaya ta ni waye har sai na fadi suna na na yi dogon bayani sannan a gane ni.


Amma a yanzu duk inda zan je nakan hadu da mutane na kirki da daraja suna gani na suna yabawa a kan wani abu da nake yi, suna kuma nuna ina ƙoƙari wajen isar da sako. To gaskiya wannan abubuwa ne da nake samun alheri da su.


Saboda haka ya kamata masu kallo su rinka bayar da gudummawa, don haka su gane ba kowanne shirme za a kawo musu su rinka bibiya suna kalla ba, saboda ka bata tsawon lokaci kana kallon abu marar amfani gara ka samu karamin Lokaci wajen kallon abin da zai amfani rayuwar ka ta duniya da lahira, inji Bifa."

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!