Abinda ya faru yau a birnin Niamey na Jimhuriyyar Nijar inda masu zanga zanga suka dinga ambatar sunan shugaban Najeriya suna aibata shi tare da yin zanen hotunansa suna munana shi su sani, wannan babban abin kunya ne da takaici, zagin Shugaba Tinubu a wajen 'yan Nijar su sani zagin dukkan 'yan Najeriya ne, domin a yanzu haka Bola Ahmed Tinubu shi je shugaban dukkan 'yan Najeriya.
Abinda suka yi ya saɓa da ƙa'idar 'yan uwantaka da kuma mutuntaka dama maƙwabtaka. Ya kamata mutanan Jimhuriyyar Nijar su sani saɓani ba aibu bane. Akwai wata ƙa"ida ta rayuwa da ta ke cewa:
“Zan iya faÉ—a da É—an uwana, amma akansa zan iya faÉ—a da duniya”. Wannan shine taken ‘yan uwantaka. Sabani a tsakanin ‘yan uwa É—abi’a ce da É—an Adam ba ya iya guje mata, sai dai abin so shi ne kiyayewa da kuma É—aukar matakin sassauta saÉ“anin domin wanzuwar ‘yan uwantaka.
Najeriya (musamman Arewa) da Jimhuriyyar Nijar ‘yan uwa ne da suka haÉ—u a wasu abubuwa da yawa, kama daga addini, al’ada, harshe, kasuwanci, kan iyaka, tarihi da zumuncin auratayya. A É—abi’ance waÉ—annan sune abebaden da suka fi haÉ—a kan bani-adama.
A É—abi’ance, abu ne maimatuÆ™ar wahala a ga Æ™ani ya fito duniya yana cin zarafin wansa saboda wani saÉ“ani da ya shiga tsakaninsu, duk saÉ“anin da ba za a iya sulhunta shi a cikin gida ba, ba shakka babu amfanin fitowa da shi duniya a yayata shi matuÆ™ar sulhu da fahimtar juna ake nema. Saboda haka, ba zai zo da mamaki ba idan makwabtan juna suka samu sabani, sai dai babban abin nema a irin wannan hali shi ne, nuna dattako, sanin ya kamata da hangen nesa domin akwai gobe.
Amma sam shugabannin mulkin sojan Nijar basu san haka ba, sun yi amfani da jahilcin mutanansu suka ingazasu akan ƙiyayyar mutanan Najeriya, domin zagin shugaban Najeriya zagin baki ɗayan 'yan Najeriya ne. Allah yasa su gane.
Yasir Ramadan Gwale
28.12.2024
Post a Comment
0Comments