Zargin da Ƙasar Nijar tayi akan Najeriya baya da tushe bare makama - Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Najeriya tayi fatali da wasu zarge-zarge da shugaban Mulkin Soji na Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani yayi a cikin wani faifan Bidiyo da ya karaÉ—e kafafen Sada zumunta, akan wata yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Najeriya da Faransa akan tsaro.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan Jama'a na ƙasa Mohammed Idris ne ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin da na dandalin Facebook.
Yace waɗannan zarge-zarge ba komai bane face zato da hasashe Maras kyau, yana mai jaddada cewa, Najeriya bata da wani shiri na haɗa hannu da wata ƙasa, don ɗaukar nauyin ƴan Ta'à dda domin dagula harkokin mulki a ƙasar Nijar.
Post a Comment
0Comments