ÆŠaliban Kwalejin Kimiyya Lafiya ta Jihar Kebbi da ke Jega sun koka da halin da makarantar ke ciki tsawon watanni tun bayan rufeta da aka yi watannin baya sakamakon bore da wasu daga cikinsu su ka yi kan zargin shugabannin kwalejin da rashawa.
Waɗanda galibinsu a yanzu haka su na zaune a gidajen iyayensu ba tare da samun wani abin yi ba, ɗaliban sun yi ƙira ga gwamnatin Jihar Kebbi da ta sake waiwaiyar lamarin makarantar tare da buɗewa ko za su samu komawa karatu daga farkon watan Janairun 2025 da za a shiga.
Post a Comment
0Comments