Halin Kunci: Dangote Ya Sake Tausayawa Al'umma, Ya Rage Farashin Mai a Najeriya
Daga: YANCI HAUSA NEWS
Duba da halin kunci da al'umma ke ciki musamman a wanna lokaci, Matatar Dangote ta sake rage farashin mai
Kamfanin na Dangote ya dauki matakin ne duba da halin da ake ciki a Najeriya musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara
Wannan ba shi ne karon farko ba da kamfanin ke rage farashin saboda a watan Nuwambar 2024 ma ya rage zuwa N970
Matatar mai na Aliko Dangote ta sake rage farashin man fetur a Najeriya yayin da aka fara bukukuwan karshen shekara.
Kamfanin ya rage farashin mai zuwa N899 kan kowace lita domin saukakawa al'umma a wannan lokaci.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan hulda da jama'a, Anthony Chiejina ya fitar a yau Alhamis 19 ga watan Disambar 2024, karamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kamfanin ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin taimakawa 'yan Najeriya da sauƙin wahala a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
“Matatar mai a Afirka ta farko ta Dangote wanda ta rage farashin mai zuwa N970 a kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba."
"Yanzu ya sake sanar da sabon farashi na N899 a kowace lita."
"Wannan rangwamen an yi shi ne domin rage tsadar sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara da ake ciki.” - Cewar sanarwar
NNPCL ya karbi bashi domin tallafawa Dangote
A baya dai Kun ji cewa, kamfanin NNPCL ya karbo bashin dala biliyan 1 domin tallafawa aikin matatar Dangote a lokacin da matatar ta shiga wata matsala.
An rawaito cewa Mele Kyari ya jagoranci sauye-sauye a NNPCL, wanda ya kai ga samun riba a karon farko cikin shekaru masu yawa.
Post a Comment
0Comments