Kuɗin hutu na 2024:
Ma'aikatan a Soba sun yabawa Shugaban ƙaramar hukumar bisa biyansu akan lokaci
Kungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta kasa (NULGE) ta yabawa shugaban karamar hukumar Soba, Hon. Muhammad Lawal Shehu, bisa amincewa da biyansu kudin hutu na 2024 akan lokaci.
Shugaban kungiyar NULGE reshen Soba, Kwamared Abdulmalik Aliyu Shehu, ya bayyana hakan a madadin ma’aikatan karamar hukumar Soba a wata takardar godiya da ya rubuta wa shugaban ƙaramar hukumar kamar yadda manema labarai suka yi tozali da ita.
Ya ce kuɗin hutun ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan yanayin tattalin arzikin kasar, yana mai cewa wannan karamcin zai ba su damar yin bukukuwan kirsamati da sabuwar shekara cikin annashuwa tare da iyalansu.
“Biyan kudin hutun ya zo akan gaɓa da ake bukata, kuma muna godiya da wannan karamci tare da iyalanmu da hakan ke nuna yadda kake sane da sadaukarwa da ma'aikata ke nunawa cewa bai tafi a banza ba. Muna alfahari da hakan", cewar Shugaban NULGE.
Idan dai ba a manta ba, kwanaki kadan bayan shigarsa ofis a watan Nuwamba, shugaban karamar hukumar Soba ya amince da biyan kudin hutun shekara ta 2023 ga ma’aikatan karamar hukumar.
Haka ma a farkon watan Disamba, Shugaban ya kuma tallafa wa ma’aikatan ƙaramar hukumar a lokacin jarabawar karin girma ta na'ura mai ƙwaƙwalwa ta 2024 da aka shirya ga ma’aikatan kananan hukumomi.
A don haka Hon Muhammad Lawal Shehu ya yi wa daukacin ma’aikatan ƙaramar hukumar barka da hutun kirsamati da kuma sabuwar shekara.
Post a Comment
0Comments