NNPP Ta Yi Fatali Da Yunkurin Kama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Dawakin-Tofa
Daga: YANCI HAUSA NEWS
Jam’iyyar, NNPP, ta yi Allah wadai da cin zarafi da yunkurin cafke babban daraktan yada labarai da wayar da kan Jama'a na gwamnatin jihar Kano, Malam Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano, Sakataren Yada Labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya ce hukumomin ‘yan sanda, bisa ga dukkan alamu suna bin umarnin Abuja, suna ci gaba da kokarin cafke Dawakin-Tofa duk da umarnin kotu da ya hana ‘yan sandan Najeriya daukar wannan mataki.
Johnson ya fayyace cewa yunkurin da aka yi na kama Dawakin-Tofa, tare da cin zarafin ‘yan uwansa, ya samo asali ne daga wata takardar koke da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya rubuta masa ko kuma daidaikun mutane masu yin aiki a madadinsa.
Kakakin jam’iyyar NNPP ya yi tir da matakin da ‘yan sandan suka dauka, yana mai bayyana su a matsayin cin zarafi ga bin doka da oda da kuma cin zarafi a fili.
Ya bayyana cewa an tilastawa Dawakin-Tofa boyewa ne a matsayin wani mataki na kariya daga abin da ya kira kama shi ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa: “Kamar yadda jama’a ke gani, al’amura a Kano a yanzu sun rikide zuwa rudani tare da yin amfani da irin wannan cin zarafin jami’an gwamnatin jihar. Lamarin yana da matukar damuwa da rashin tausayi.
"Kuma wannan, ya fito ne daga wata jam’iyya da ke yin kaca-kaca da cewa za ta iya jawo masu zuba jari daga kasashen waje zuwa kasar.
"Masu saka hannun jari nawa ne za su zaÉ“a su yi aiki a cikin al’ummar da ake cin zarafin doka da Æ™aƙƙarfan cibiyoyi da ake son tabbatar da ita?
“Tunda akwai umarnin kotu da ya hana ‘yan sanda, yunkurin da aka yi na kama Sanusi ya jefa mumunan batanci ga martabar ‘yan sandan Najeriya.
"Abin takaici ne game da irin wannan aika-aikar da aka yi a lokacin da ake yin nadama a kan mulki a Kano kan batun masarautau, Watakila, a wani lokaci, jam’iyya mai mulki za ta gane irin yadda shugabancinsu ya bata sunan su, musamman a Arewacin Najeriya.”
NNPP ta yi kira ga Sufeto-Janar na ’yan sanda
Jam'iyyar ta yi kira ga, Kayode Egbetokun Sifeton yan sanda na kasa, da ya tabbatar da cewa ‘yan sanda a matsayinsu na cibiya, sun bijire wa ruguza masu hatsarin gaske cikin siyasar bangaranci.
Jam’iyyar ta kuma bukace shi da ya hana jami’ansa ci gaba da cin zarafi da tursasawa da ake yi wa Dawakin-Tofa, wanda ta jaddada hakkinsa na dan Adam a karkashin doka kuma dole ne a mutunta shi.
Post a Comment
0Comments