RASHIN KYAKYAWAR ALAKA TSAKANIN GWAMNATI DA TALAKAWA NE YA KARA TA'AZZARA MAGANAR SHUGABAN NIJAR
~~ Daga Shehu Jaha
Wato idan kuka karewa zarge-zargen Shugaban kasar Nijar kallo kan Gwamnatin Tarayya zaka fahimci ko akwai gaskiya ko babu Talakawan kasarnan baza su iya marawa Tinubu baya ba.
Nayi imani da akwai kyautatawa tsakanin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da Talakawan kasarnan da su ne zasu taya shi fada da maganganun Janar Abdulrahaman.
Maganganun nasa sun zo lokacin da Talakawa ke karbar wuta babu Babba babu Yaro, Kuma dama a Wuya ake da Gwamnatin musamman kan wahalhalun rayuwa da batun tsaro.
Ko kadan ban yi imani da maganganun Shugaban Nijar ba to amma ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fito tayi gamsashshen bayani.
Haka Kuma wannan ya kamata ya zamewa Gwamnatin Tarayya izina, cewar mutane zasu iya gamsuwa da ko wane irin zargi idan aka dorawa Gwamnatin ko kuwa ba gaskiya bane.
Post a Comment
0Comments