SANATA UBA SANI YA CIGABA DA KADDAMAR DA SABBIN TITUNAN MOTA DAYA SAMAR A JIHAR KADUNA - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 SANATA UBA SANI YA CIGABA DA KADDAMAR DA SABBIN TITUNAN MOTA DAYA SAMAR A JIHAR KADUNA


Domin cika alkawuran daya daukarwa al'ummar Jihar Kaduna, Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani, ya kaddamar da sabbin titinan Mota guda 12.


Titunan daya kaddamar yau Suma daga cikin Titunan Motoci 70 manya da matsakaita Wanda suka Kai adadin kilomita 770 a dukkanin fadin yankunan Jihar Uku, a kananan hukumomi 23.


Hanyoyin sune kamar haka: 


i. Titin Ja Abdulkadir 

 ii. Hanyar Bissau 

 iii. Titin Unguwan Muazu 

 iv. Hanyar Shan-Ruwa 

 v. Titin Layout dake daura da Titin Yakubu Gowan 

 vi. Titin Yan Awaki dake Kawo

 vii.Baban titin dake shataletalen filin wasanni

 viii. Filin wasa zuwa Tasha Roundabouts 

 ix. Madaidaitan titinan a Gobarau road

 x. Tituna a Kinshasa 

 xi. Hanyar Sultan-Surame 

 xii. Titin Ohinoyi


 A lokacin da yake kaddamar da ayyukan titunan, Sanata Uba Sani ya jaddada manufar Gwamnatin sa na cigaban gudanar da ayyukan cigaba a dukkanin fadin Jihar musamman a yankin Karkara.







Gwamna, Uba ya ce titunan zasu saukaka dukkanin zirga-zirgan al'ummar Jihar Kaduna, ta fuskar kasuwanci, zuwa neman lafiya, ayyukan gona da tsaro zuwa neman ilimi da sauran su.


Ya ce a tsakanin watanni 3 zuwa 6 na shekarar mai kamawa ta 2025, zai sake kaddamar da sabbin hanyoyi a shiyyoyi uku na jihar Kaduna.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!