Shekararka 40 kuna zauna lafiya da matarka babu wanda ya taba jin kanku ko menene sirrin?
Ya ce: Bayan an gama ɗaura auranmu sai na ɗauki Amarya domn zuwa shaƙatawa, muka je wani waje muka hau Doki.
Kasancewar bata iya ba dokin ya bugata da ƙasa..! Ta tashi ta shafa kan dokin ta ce, ka yi na farko.
Ta sake hawa dokin, ya sake bugata da ƙasa a karo na biyu. Ta shafa kan sa ta ce, gargaɗi na 2 kenan!
A karo na uku Doki ya sake bugata da ƙasa...! Bata yi wata-wata ba ta ɗakko KULKI ta bugawa dokin a kansa, take dokin ya mutu.
Na taso ina yi mata faÉ—a, ina tsawa na ce, kina da tabin hankali ne...!
Ta kusanto ni a tsanake ta kalle ni tana murmushi tana shafa kaina tana cewa, Habibi k yi mini tsawa, kuma ka zage ni, wannan shi ne karo na farko....!
Tun daga wanan ranar muke rayuwa cikin nutsuwa da jin daÉ—i da kuma kaffa-kaffa domin kar ma a yi kuskure har mu kai ga gargaÉ—i na biyu...!
Post a Comment
0Comments