Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutu bayan Gabatar da Kasafin Kudin 2025
Daga: YANCI HAUSA NEWS
Shugaban ƙasan Najeriya ya tafi hutun bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara a jiharsa ta Legas da ke yankin Kudu maso Yamma
Mai girma Bola Tinubu ya isa Legas ne da rana jim kaÉ—an bayan ya kammala gabatar da kasafin kuÉ—in shekarar 2025 a gaban majalisar tarayya
Bayan isarsa filin jirgin saman Murtala Muhammad, ya samu tarba daga wajen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu da sauran ƙusoshin gwamnati
Shugaba Bola Tinubu ya isa jihar Legas domin hutun bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Shugaba Tinubu ya isa filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas, da misalin ƙarfe 3:23 na rana a ranar Laraba.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya fitar, a cewar rahoton jaridar The Punch.
Dada Olusegun ya sanya bidiyon tarbar da aka yi wa Shugaba Tinubu a filin jirgin saman Murtala Muhammad a shafinsa na X.
Kafin ya bar Abuja, shugaban ƙasan ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga majalisar tarayya domin tantancewa tare da amincewa da shi.
Tinubu ya isa Legas domin hutu
Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya samu tarba daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, mataimakin gwamna Obafemi Hamzat da ƙusoshin gwamnati a filin jirgin.
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa jihar Legas domin gudanar da hutun bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara."
"Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, mataimakin gwamna, Obafemi Hamzat, da mambobin majalisar zartarwa sun tarbi shugaban ƙasan a filin jirgin saman Murtala Mohammed."
"Kafin ya tafi Legas, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuÉ—in 2025, wanda ya kai N47.9trn, a gaban wani taron haÉ—in gwiwa na majalisar tarayya a Abuja."- Bayo Onanuga
Post a Comment
0Comments