Tashin Wata Mummunar Gobara A Kasuwar Babura Ya Haifar Da Asarar Dubin Dukiya - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 Tashin Wata Mummunar Gobara A Kasuwar Babura Ya Haifar Da Asarar Dubin Dukiya




Daga: YANCI HAUSA NEWS 


An samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar Babura ta ‘Yan-Dole da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.


An tattaro cewa lamarin wanda ya faru a yammacin ranar Asabar, ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici, yayin da shaguna da rumfuna da dama suka kone kurmus.


A cewar shaidun gani da ido, gobarar, wacce har yanzu ba a iya gano musabbabin ta shin ta ba, ta bazu cikin sauri a kasuwar da ke zama cibiyar hada-hadar babura da kayayyakin gyara a jihar.


“Ba mu san musabbabin tashin gobarar ba, kawai mun lura da wuta daga shagunan baburan na ci, amma jami’an kashe gobara na ci gaba da kokarin kashe ta,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa manema labarai.


An ce da dama daga cikin ‘yan kasuwa da masu shaguna sun yi ta yunkurin kwato kayayyakinsu cikin hayyacinsu amma ba su samu ba saboda zafin wutar da ta ke ci.


A halin da ake ciki kuma, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara sun isa wurin jim kadan bayan da gobarar ta tashi tare da kokarin shawo kan gobarar.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!