Dalilin Korar Yan Kasar Ghana Daga Najeriya 1983 Da Yadda GHANA MUST GO Ta Samo Asali
Fitar da 'yan Yammacin Afirka daga Nijeriya Ya faru bayan umarnin zartarwa a 1983 daga Shugaban Najeriya Shehu Aliyu Shagari wanda aka tilasta wa baƙi su bar kasar 'Sakamakon na odar Shagari, sama da Yan kasashen Afirka ta Yamma miliyan biyu aka kora" ciki har da 'yan kasar Ghana miliyan Daya.
Jama’ar Kasar Ghana mazauna Najeriya a shekara 1983 wanda yawan su ya kai mutum Miliyan daya, Najeriya tayi zargin cewa yawancin bakin haure ne. Kuma A Lokacin ba a jima da gama rikicin Maitsine ba!. Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa da Akwai Yan Kasashen Yammacin Afirka a cikin almajiran Maitatsine da su ka tayar da tarzoma a Kano a karshen Shekarar 1981. Wannan hukunci da kasar Najeriya ta dauka ya girgiza duniya.
Yan Najeriya sun yi murna matuka lokacin da aka sanar da wannan da korar, su kuwa yan Ghana Wannan bacin rai ne da ba zasu taba mantawa ba.
A Ranar 10 Ga Watan Mayu Na Shekarar 1983, Gwamnatin Najeriya ta Fitar da Sanarwa Ko dai Yan Ghana Su Fice Daga Kasar Ko su Fuskanci Kamu Da Gabatar Dasu A Gaban Kotu Da Shan Dauri. A Najeriya an rika cika manyan Motoci da Jiragen ruwan daukar kaya da yan Ghana, sa’annan aka sanya Sojoji da su sa ido, su tabbatar kowannen su ya bar Najeriya.
Yawancin Yan Ghana sun tafi sun bar Kadarori da Arzikin su saboda rashin samun takardun zama daga Gwamnatin Najeriya.
Gwamnatin kasar Ghana ta wannan lokacin tayi tofin Allah tsine da nuna bacin rai ta ce “Najeriya ta ji kunya!!!
Wannan mataki da Najeriya ta dauka ya saba da tsarin kungiyar hadin kan kasashen Afirka” ta OAU, nan da nan Kalmar ‘Ghana must go’ ya zama abin raha tsakanin yan Najeriya, su na ganin Gwamnatin Shagari tayi abin daya kamata. Sun sa ran cewa korar mutanen Ghana daga Najeriya zai kawo mu su samun aikin yi.
IDAN ZA A YI TAFIYA DOLE A NEMI JAKA.
Wannan Dalili Ne Ya Sanya, "Yan Ghana Nemo Manyan Jakukkuna Domin Zuba Kayayyakinsu.
Post a Comment
0Comments