Yansanda sun kama kusa a Jam’iyyar NNPP a Borno - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 ‘Yansanda sun kama kusa a Jam’iyyar NNPP a Borno bisa zargin sukar Gwamna Zulum


Rundunar ‘YanSandan Jihar Borno ta kama wani jigo a jam’iyyar NNPP, Atom Magira, bisa zargin sukar Gwamna Babagana Zulum.

Hadimin Mr. Magira, Mohammed Yahaya, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun dauke shi ne a daren Lahadi.


DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Magira, wanda ya taba neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2019, yana daga cikin manyan ‘yan adawa a jihar. Ya kasance mai magana sosai kan wasu manufofin Gwamna Babagana Zulum.


Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an kama Mr. Magira ne saboda wani allon talla da magoya bayan “YES TO MERGER” suka dauki nauyi, suna kira da a hada kan dukkan jam’iyyun siyasa a jihar.


Allon da aka rubuta “Say Yes To Merger” tare da hoton Mr. Magira daga baya an lalata shi ba tare da sanin wanda ya yi hakan ba.


“Gwamnatin jiha ce ta bayar da umarnin, ba sa son ganin wata babbar adawa a jihar. Duk wanda ya yi hakan za a takura masa, hakan ya zama ruwan dare tun daga 1999, amma Magira ya ci gaba da kasancewa mai kawo adawa mai ma’ana a Jihar Borno,” in ji wata majiya.



“Har yanzu Magira yana tsare a safiyar Litinin, amma ba a tabbatar ko za a gurfanar da shi a kotu ba,” wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ta ce wa wakilin Daily Nigerian.


Kakakin rundunar ƴansanda a jihar Borno, Nahum Kenneth Daso, ba a samu jin ta bakin sa ba kan lamarin.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!