Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Sake Bai wa Musa Iliyasu Kwankwaso Mukami mai Tsoka
Daga: YANCI HAUSA NEWS
Shugaban Æ™asa Bola Ahmad Tinubu ya amince da nada Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin Daraktan KuÉ—i na hukumar raya kogunan Hadejia -Jama’are mai kula da Kano.
Kafin wannan nadin Musa Iliyasu Kwankwaso mamba ne a Majalisar Ƙoli ta wata makarantar gaba da sakandire dake jihar Kogi.
A baya da Musa Iliyasu Kwankwaso ya rike mukamin kwamishina har sau uku a gwamnatin jihar Kano, Inda ya yi aiki da Malam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje.
Idan za a Iya tunawa Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban Æ™asar ya nada Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayin Manajan daraktan Kogunan Hadejia – Jama’are mai kula da Kano.
Post a Comment
0Comments