Ɗan gidan Ministan Abuja, Nyesom Wike, Jordan ya kammala karatun digirin digirgir a bangaren Shari’a (LLM) a Jami’ar Queen Mary, dake Birnin Landan, UK
Wike ya bayyana wannan labari mai daɗi a shafinsa na sada zumunta, inda ya rubuta:
“Na yi farin ciki tare da matata wajen halartar bikin yaye ɗanmu, Jordan, wanda ya kammala digirin Master na Shari’a (LLM) a Jami’ar Queen Mary ta London, UK.
A matsayina na uba, ina farin ciki da cigaban da Jordan ke samu wajen bin tafarkin sana’arsa.”
Post a Comment
0Comments