Bola Tinubu ya zo na uku cikin jerin masu cin hanci da rashawa na duniya, da masu aikata laifuka na shekarar 2024
Kungiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP), wata ƙungiya ce ta binciken masu cin hanci da rashawa da masu aikata laifuka ta duniya, kungiyar ta sanar da jerin sunayen manyan mutane masu cin hanci na shekarar 2024. A wannan jerin, an sanya sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Wanda shine ya zo na uku a cikin jaddawalin.
OCCRP ta gudanar da zaÉ“en ne ta hanyar karÉ“ar Æ™uri’u daga mutane daban-daban a duniya, don gano wadanda suka taka rawa sosai wajen haÉ“aka cin hanci, rashin gaskiya, da Æ™ara talauci a Æ™asashen su.
A jerin wannan shekara, Shugaba Tinubu ya samu matsayi na uku, bayan tsohon shugaban Indonesia, Joko Widodo. Shugaban Kenya, William Ruto, ne ya samu Æ™uri’u mafi yawa a jerin. Amma babban lambar yabo ta "Person of the Year" an ba tsohon shugaban Siriya, Bashar al-Assad, wanda aka ce ya gudu zuwa Rasha bayan shekara da shekaru yana sace dukiyar Æ™asarsa.
Post a Comment
0Comments