Gwamnatin kwadebuwa ta sanar da janyewar sojojin Faransa a fadin kasar.
A cewar sanarwar “Mun yanke shawarar janye sojojin Faransa ta hanyar da aka tsara cikin tsari,” in ji Shugaba Alassane Ouattara a cikin wani jawabin da yayi a gidan talabijin.
A jawabin sabuwar shekara da ya gabatar, Shugaban Côte d'Ivoire, Alassane Ouattara, ya sanar da cewa za a fara janye sojojin Faransa daga ƙasar nan ba da jimawa ba.
Ya ce, “Mun yanke shawarar janye sojojin Faransa ta hanyar da aka tsara cikin lumana.”
Shugaban ya bayyana cewa janyewar za ta fara a watan Janairu, tare da ambaton ci gaban karfafa dakarun sojin Côte d'Ivoire.
Shugaban ya kuma kara da cewa sansanin dakarun ruwa na Faransa da ke Port Bouet za a mika shi ga sojojin ƙasar.
A halin yanzu, akwai kusan sojojin Faransa 600 da ke Côte d'Ivoire.
A baya, wasu kasashe na Yammacin Afirka kamar Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar sun bukaci Faransa ta janye sojojinta daga yankin.
Hakan na nuni da cewa ƙarshen mulkin mallakar Faransa ya zo karshe a yankin Nahiyar Afirka, ƙasar ta ci gaba da kasancewa da sojojinta a yankin.
musamman a yaÆ™in da ake yi da 'yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi.
A halin yanzu cibiyoyin sojojin Faransa da suka rage a nahiyar Afirka za su kasance ne kawai a Gabon da Djibouti da ke gabashin Afirka.
Post a Comment
0Comments