Gamayyar kungiyoyin fararen hula CSO sun ayyana Ministan Tsaro Matawalle a matsayin gwarzon Ministan 2024
Gamayyar kungiyoyin fararen hula 774 ta ayyana Dr Bello Muhammad Matawalle, ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya a matsayin "Gwarzon Ministan shekarar 2024".
Hakan ya biyo bayan la'akari da irin jagoranci na musamman, sadaukar da kai ga tsaron Nijeriya, da kuma nasarorin da ya samu a duk a shekarar 2024 da ke shirin karewa.
Shugaban kungiyar na kasa Dr Hakeem Baba Tunde ne ya sanar da hakan a ranar Talata a cikin wata sanarwa. A cewar Baba Tunde, Dr Matawalle ya kasance yana mayar da hankali ne a kan harkokin diflomasiyya da hadin kan cikin gida biyu, wanda ya haifar da gagarumin ci gaba a tsarin tsaron kasar.
Ya ce, “Dr. Matawalle ya fara ne a shekarar 2024 tare da mai da hankali kan bangarori na harkokin diflomasiyya da hadin guiwar cikin gida, daga ranar 8-9 ga watan Janairu, ya fara ziyarar aiki kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Janar Christopher Gwabin Musa, a yayin ziyarar, sun kulla alaka da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, domin inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
“A ranar 20 ga watan Janairu, ya halarci sansanin sojin saman Nijeriya na socio-Cultural Activities BASA na Nijeriya a shekarar 2023 a Abuja, wanda Air Marshal Hassan Bala Abubakar ya karbi bakunci, inda ya yi bikin sadaukarwar mayakan sama da mata. Bayan kwana biyu, ranar 22 ga watan Janairu, Dr. Matawalle ya karbi bakuncin mai martaba Salem Saeed Al-Shamsi, Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Nijeriya, domin tattaunawa kan zurfafa tsaron Nijeriya da kyautata alakar kasar UAE da Nijeriya.
“Ya kammala wannan wata ne da wani taron kwana biyu a ranakun 24-25 ga watan Janairu, domin magance matsalolin tsaro da Arewacin Nijeriya ke fuskanta, gamayyar kungiyoyin Arewa CNG ne suka shirya taron a cibiyar samar da kayan aikin soja ta Nijeriya da ke Abuja.
“A cikin watan Fabrairu, huldatayyar da Dr. Matawalle ke yi da kasashen duniya ta kai shi Riyadh, Saudi Arabia, inda ya halarci baje kolin tsaro na duniya daga 4-8 ga Fabrairu.
"Bikin ya nuna karfin tsaron Nijeriya tare da duba dabarun hadin guiwa. A ranar 23 ga watan Fabrairu, ya karrama jami'an tuta da suka yi ritaya na rundunar sojojin ruwan Nijeriya a Asokoro, Abuja.
“Maris wata ne na shirye-shirye masu tasiri, a ranar 4 ga Maris, Dr Matawalle ya tattauna da Mrs. Hen Cohn, Daraktar Hukumar Kula da Ma’adanai ta Majalisar Dinkin Duniya (UNMAS), don kafa cibiyar kula da ma’adanai a Maiduguri don inganta tsaro a wuraren da ake fama da rikici.
“A ranar 6 ga Maris, tare da hadin guiwar Yarima Shu’aibu Abubakar Audu, Ministan tama da karfafa, suka aza harsashin farfado da kamfanin karafa na Ajaokuta, domin karfafa samar da kayan aikin soja, a ranar 7 ga Maris, ya kara kulla alaka ta tsaro tsakanin kasar Indiya da Nijeriya, taron hadin gwiwar tsaro a Abuja.
“Daga baya a cikin watan, a ranar 19 ga Maris, ya jagoranci taro na 34 na Hukumar Gudanarwar Defence Health Maintenance Limited. A ranar 26 ga Maris, ya ba da gudummawa wajen tace dabarun tsaron Nijeriya a babban taron kwamandojin hadin guiwa na rundunar sojojin Nijeriya a Abuja.
"A ranar 27 ga Maris, tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Dr Bello Matawalle ya halarci wani gagarumin biki na jana'izar sojojin da aka kashe a lokacin da suka yi wa kasarsu hidima a Okuama."
“A watan Afrilu an gudanar da muhimman abubuwa, ciki har da halartar Dr. Matawalle a wajen kaddamar da jirgin sintiri na rundunar sojojin ruwa ta Nijeriya a Turkiyya a ranar 19 ga Afrilu, a ranar 22 ga Afrilu, ya bi sahun Shugaba Tinubu a wajen taron yaki da ta’addanci na Afirka da aka yi a Abuja, inda ya jaddada shugabancin Nijeriya wajen magance tsaron matsalar tsaron yankin.
"A ranar 23 ga Afrilu, ya karbi bakuncin ministar tsaron kasar Mauritania, Hanena Ould Sidi, domin inganta hadin guiwar tsaron kasashen biyu, a ranar 27 ga watan Afrilu, ya halarci bikin yaye sabbin sojojin ruwa a kwalejin horar da sojojin ruwa ta Nijeriya da ke Onne, jihar Rivers.
“Dr Matawalle ya kammala wannan wata ne a ranar 30 ga Afrilu, inda ya karbi bakuncin tawagar ma’aikatar tsaron Amurka, karkashin jagorancin mataimakiyar sakatariyar Mrs Jennifer Zakriski, domin tattaunawa kan muradun tsaron juna.
“Daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Mayu, Ministan ya halarci bikin cikar rundunar sojojin saman Nijeriya shekaru 60 a Abuja da Kaduna, a ranar 28 ga watan Mayu, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da sabuwar dokar masana’antun tsaro ta Nijeriya (DICON) tare da duba kayayyakin aiki a Abuja. Hedikwatar Hukumar Leken Asiri ta Defence A ranar 29 ga Mayu, ya bi sahun Shugaba Tinubu wajen bikin gyaran hanyar jirgin kasa na Abuja.
“A ranar 12 ga watan Yuni, Dr. Matawalle ya halarci faretin ranar dimokuradiyya karo na 25 a dandalin Eagle Square, Abuja, wanda ke nuna 'sulisin' karni na tafiyar dimokuradiyyar Nijeriya.
"A ranar 4 ga watan Yuli, ministan ya jagoranci taron farko na majalisar gudanarwar hukumar kula da ruwa ta kasa, inda aka mai da hankali kan harkokin tsaron teku, a ranar 18 ga watan Yuli, ya yi nazari kan hadin guiwar kera kayayyakin tsaro tare da tawagar hukumar shigo da fasahohin jiragen sama ta kasar Sin CATIC.
“A cikin watan Agusta, Dr Matawalle ya halarci taron shugabannin kungiyar ECOWAS da aka yi a Abuja ranar 8 ga watan Agusta, a ranar 14 ga watan Agusta, ya kaddamar da shirin samar da harsasai na gida a bikin cika shekaru 60 na DICON, a ranar 20 ga watan Agusta, ya kaddamar da dakin binciken cutar tarin fuka a barikin soji mai suna Mogadishu.
“A watan Satumba ne Dr Matawalle ya kara zage damtse wajen magance matsalar ‘yan bindiga a Sokoto, biyo bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar, ya gudanar da ayyukan tsaro da kuma duba wuraren da abin ya shafa, inda ziyarar tasa, ta haddasa kisan Alhaji Halilu Sububu tare da kashe dubban ‘yan bindiga a Sokoto da Zamfara da sauran sassan kasar.
“Ziyarar sa ta biyu a Sokoto daga ranar 8-12 ga Oktoba ta hada da tantance wuraren aikin soji da ayyukan tsaro a garuruwan Gundumi, Tsamaye, Isa, Goronyo, Mai Lalle, da sauran kauyukan da ‘yan fashin daji suka shafa, a ranar 15 ga Oktoba, ya karrama marigayi Laftanar Janar Lagbaja a makabartar sojoji ta kasa.
“A watan Nuwamba, Dr. Matawalle ya halarci taron kara wa juna sani na sojojin ruwa na Gulf of Guinea a ranar 27 ga watan Nuwamba, inda ya karfafa hadin guiwa a fannin tsaro a teku. A watan Disamba, Dr Bello Matawalle ya ziyarci asibitin sojoji 44 da ke Kaduna a ranar 7 ga Disamba. A ranar 12 ga Disamba, ya tarbi mataimakin sakataren harkokin tsaron Amurka. Sannan a ranar 29 ga Disamba, ya wakilci Shugaba Tinubu a taron ayyukan zamantakewa na Afirka ta Yamma (WASA).
A ranar 20 ga watan Nuwamba Mataimakin Ministan tsaron Saudi Arabia Yarima Abdurrahman bin Mohammed bin Ayyat ya karbi bakuncin Minista Bello Matawalle a birnin Riyadh, inda suka tattauna hanyoyin inganta tsaron kasashen biyu.
Dr. Bello Matawalle ya kuma kai ziyara a jihar Zamfara da zummar kai agaji fa tattalin arzikin al'ummar yankin, ciki kuwa hada albishirin cewa za a kafa sansanin sojin ruwa a yankin karamar hukumar Maradun ta jihar. Bugu da kari, Dr Matawalle ya shige gaba don ganin an gina katafaren asibiti na Naira bilyan 2.25 a garin na Maradun don inganta lafiyar al'ummar yankin da ma na jihar baki daya. Wadannan nasarori da ma wasu da lokaci bai ba mu damar ambata ba, su ne waÉ—anda mai girma Ministan tsaron Nijeriya Dr Bello Matawalle ya samu a shekarar 2024 da ke shirin ban kwana.
Kungiyar ta jaddada cewa an bayar da wannan lambar yabon ne bisa cancanta kawai. “Dr Matawalle ba ya da wata masaniya kan abin da muka shirya. Ba mu ma taba haduwa da shi Ido da ido ba, amma mun bi diddigi da nazarce-nazarcen da suka sa muka samu wadannan bayanai a cikin shekarar,” in ji Baba Tunde.
A yayin da Najeriya ke neman shiga shekarar 2025, gamayyar kungiyoyin sun yaba da gudunmawar da Dr Matawalle ya bayar wajen tabbatar da tsaron kasa da ci gaban hadin guiwa a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.
Post a Comment
0Comments