Tinubu ya amince da bawa tsofaffafin janar dala dubu ashirin $20000 - YANCI HAUSA NEWS

YANCI HAUSA
By -
0

 Tinubu ya amince da motoci masu sulke da kuma tafiya duba lafiya ga Janarorin Soja da suka yi ritaya



Wasu daga cikin alawus-alawus din sun haÉ—a da bayar da mota mai sulke (bulletproof SUV) a matsayin kyautar ritaya, tare da biyansu makudan kudade na magani a Æ™asashen waje. 


tare da basu Dala dubu $20,000 a matsayin kuÉ—in tafiya (estacode) tafiya dubu lafiyarsu, da kuma biyan ma’aikatan gida kamar masu dafa abinci da masu aiki a gida.


Sabuwar dokar Harmonised Terms and Conditions of Service for Officers and Enlisted Personnel in the Nigerian Armed Force an tsara ta ne tun zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an rattaba hannu a kanta daga shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar 14 ga Disamba, 2024.


Dokar ta fara ne da manyan shugabannin rundunar sojoji, inda ta tanadi cewa Shugaban Tsaron Ƙasa (Chief of Defence Staff), Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa (Chief of Army Staff), Shugaban Rundunar Sojin Ruwa (Chief of Naval Staff), Shugaban Rundunar Sojin Sama (Chief of Air Staff), da sauran manyan jami’ai suna da haƙƙin samun mota mai sulke ko makamancin ta a matsayin kyautar ritaya.


Hakazalika bayan mota mai sulke tare da ƙarin wasu motoci masu rakiya, dokar ta ce "duk bayan shekaru huɗu, za'a sauya musu wasu ko a sake musu gyara.


A cewar dokar wannan kudin zai rika fita ne daga asusun Rundunar sojin Najeriya don kula da tsofaffin Janarorin. 


Bayan haka, janarorin da suka yi ritaya za su amfana da wasu jin daÉ—i na alfarma, ciki har da ma’aikatan gida da masu tsaron gida.


Rahoton ya bayyana cewa Laftanar Janar (Lieutenant Generals) da makamantansu za su rika samun magani a ƙasashen waje da kuma $20,000 a duk shekara, yayin da ake sa ran na Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS) zai fi haka yawa.

Tags:

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!