Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta bukaci a gaggauta maido da ma’aikata kusan 900 da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KEDC) ya kora daga aiki ba tare da wani sharadi ba.
A wata sanarwa da kungiyar ta NLC ta fitar a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugaban yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar ta NLC, Benson Upah, kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kungiyoyin ta na jihar Kaduna da su shiga zanga-zangar da ake yi domin nuna hadin kai.
Post a Comment
0Comments